'Yan bindiga sun kashe Kiristoci Kibdawa 23 a Masar

Taswirar Masar

A kalla mutum 23 aka kashe bayan da wasu 'yan bindiga suka kai hari kan wata motar safa da ke dauke da Kirista Kibdawa a tsakiyar kasar Masar.

Lamarin ya faru ne a jihar Minya mai kilomita 250 (mil 155) kudu da birnin Alkahira, a daidai lokacin da Kibdawan ke kan hanyar zuwa wani Coci.

A watannin da suka gabata, an sha kai hare-hare kan Kibdawa, lamarin da mayakan kungiyar IS suka dauki alhakin kai wa.

Ranar 9 ga watan Afrilun da ya gabata an kai wasu hare-harekunar bakin wake biyu a biranen Tanta da Iskandariya, harin da ya jawo mutuwar a kalla mutum 46.

Lamarin da ya sanya Shugaba Abdul Fattah al-Sisi kafa dokar ta-baci a kasar baki daya.

Sannan ya yi alkawarin yin duk abin da ya kamata domin tunkarar masu ikirarin jihadi.

Labarai masu alaka