Ga aikin da zai iya samar da sama da naira miliyan uku a wata

Kamfanonin sadarwa Hakkin mallakar hoto .
Image caption Yanzu hannayen jarin kamfanonin sadarwa na zamani sun fi na kamfanonin mait tsada

Shin kun san gina manhajar kwamfuta mai farin jini ka iya samar wa mutum akalla dala dubu goma, wato sama da naira miliyan uku kowane wata?

Wannan na cikin albishir din da Zubairu Dalhatu Malami, wani dan Najeriya mai kamfanin sadarwar intanet da ke hulda da kamfanin Google, ya yi wa matasan Najeriya.

Zubairu ya ziyarci ofishinmu na London ne bayan ya halarci wani taron da kamfanin Google ya shirya wanda aka yi wa lakabi da 'Google Cloud Next' da zummar wayar da kan ma'abota shafukan Intanet kan yadda za su iya amfani da rumbun adana bayanai na GOOGLE.

A hirarsa da abokin aikinmu, Aliyu Abdullahi Tanko, Zubairu ya ce: "ina tabbatar maka yanzu a Najeriya muna da mutanen da ke samun dala dubu goma (sama da naira miliayan uku) daga goggle ko wani wata."

Ya ce da yawan irin wadannan mutanen suna dakinsu ne, ba sa fita kuma ba wani rashin dai-dai suke yi ba.

"Suna zaune ne a cikin gida suna irin wannan tsare-tsaren na manhaja ta waya domin yanzu idan kana da mahaja mai kyau kuma aka sauke ta sau miliyan daya amman bai fi ace mutum dubu dari suke amfani da ita ba , toh ina tabbatar da cewa cikin yardan Allah ko mutum bai ajiye dala dubu goma (sama da miliyan uku) ba, zai ajiye dala dubu shida (sama da miliyan biyu) a ko wani wata," in ji shi.

Ya ce mutane za su iya koyar fasahar sarrafa manhajar ta kwasa-kwasai da ake yi na koyan yarukan sarrafa kwafuta.

Labarai masu alaka