Kyamar Musulmai: An kashe mutane 2 a Amurka

Muslin Hakkin mallakar hoto CBS/EVN
Image caption Harin ya aukune a cikin jirgin kasa na MAX a tashar Hollywood

'Yan sanda a birnin Portland na Amurka sun ce an kashe wasu mutane biyu, yayin da suka yi kokarin hana wani mutun cin zarafin wasu mata biyu Musulmai.

Lamarin ya faru ne ranar Juma'a a cikin jirgin kasa.

'Yan sandan sun ce mutumin wanda ya rika furta kalaman cin zarafi ga matan, ya dabawa mazan biyu wuka saboda sun yi yunkurin sa baki.

Wani fasinja guda a cikin jirgin ya samu rauni, kafin a kama maharin.

Majalisar kyautata mu'amala ta Musulunci a Amurka ta ce dole ne shugaba Trump ya dauki mataki kan yawaitar tsanar Musulunci a Amurka.

Majalisar ta zargi shugaba Trump da rura kyamar Musulmai saboda irin kalamansa da kuma manufofinsa.