Trump ya zama 'saniyar ware' cikin G7 kan dumamar yanayi

Donald Trump Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Babu shakka Mista Trump, wanda ke tare da matarsa Melania a wanna hoton, yana fatan za a yaba wa rangadinsa na farko zuwa kasashen duniya.

Mista Trump, wanda ya halarci taron na G7 a karon farko, ya taba karyata dumamar yanayi a matsayin shaci-fadi.

Duk da cewar Amurkan ta yi tarayya da sauran kasashen da suka hada da Birtaniya da Canada da Faransa da Jamus da Italiya da kuma Japan kan yaki da ta'addanci, Shugaba Trump ya ki kara shigar da Amurka yarjejeniyar dumamar yanayi ta Paris, wadda kasashen shida suka yi.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, shugaban Amurkan ya ce zai yanke shawara kan batun a mako mai zuwa.

Da yake bayani bayan tattaunawar kasashen G7 din, Firayim ministan Italiya, Paolo Gentiloni, ya ce an cimma matsaya kan wasu batuwa amma banda dumamar yanayi.

Ya ce: "Akwai batun da har yanzu ba cimma matsaya akai ba wanda shi ne batun yarjejeniyar Paris ta dumamar yanayi. Bisa wannan, shugaban Amurka da gwamnatin Amurka suna nazari kan yarjejeniyar."

Ya kara da cewar: "Sauran kasashen da suke goyaon bayan yarjejeniyar Paris ta dumamar yanayi wadda muhimmiyar aba ce ga makomarmu sun gane hakan. Muna da karfin guiwar cewar bayan wannan nazari na cikin gida, Amurka ma za ta so shige ta."

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Trump ya ki sassautawa kan shige-dafice da cinikayya da kuma dumamar yanayi

Shugabar Jamus, Angela Merkel, ta bayyana tatattaunawa kan cinikayya da dumamar yanayi a matsayin lamuran da ke cike da ce-ce-kuce, tana mai cewa ta gabatar da hujoji da dama domin kare yarjejeniyar dumamar yanayi ta Paris.

"Game da Dumamar yanayi, munyi magana da Amurka, kuma mun bayyana hujojinmu cewa muna son Amurka ta cigaba da goyon bayan yarjejeniyar dumamar yanayi," in ji ta.

Ta ce: "Ni ma da kai na bayyana cewar samun aikin yi nan gaba zai dogara ne kan amfani da albarkatu ta yadda ya dace, kuma wannan na daga cikin yarjejeniyoyin duniya kadan da kasashe masu tasowa da kasashe na tsibiri da kuma Afirka ke fatan amfana. Amman Amurka ta bayyana cewar ita ba ta yanke shawara ba, kuma ba za ta yi hakan a anan ba, amman za ta ci gaba da nazari a kansa. Amman mun tafka zazzafar muhawara, kuma sauran mahalarta taron sun mayar da hankali ne kan cewar ya kamata Amurka ta ci gaba da yarjejeniyar dumamar yanayin baya."

Mai baiwa shugaba Trump shawara kan tattalin arziki, Gary Cohn, ya ce shugaban ya halarci taron ne domin neman ilimi kuma ra'ayinsa na sauyawa kamar yadda ya kamata.

Amman Sakatare Janar na na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres wanda ya halarci taron a Sicily, ya shaida wa BBC Cewar ko wace matsaya Trump ya dauka yarjejeniyar za ta tsira.