Nigeria: 'An kammala aikin ruwan Zaria'

Hakkin mallakar hoto KADUNA STATE GOVERNMENT
Image caption An kwashe shekaru gwamnatoci na alkawarin samarwa al'ummar yankin da ruwan sha.

A Najeriya, wata matsala da ta dade tana ciwa al'mmomin yankin Zaria na jihar Kaduna tuwo a kwarya ita ce ta rashin ruwan Famfo.

An dai kwashe shekaru gwamnatoci na alkawarin samarwa al'ummar yankin da ruwan famfo, amma shiru kake ji.

Sai dai yayin da gwamnatin APC a kasar ke cika shekaru 2 akan karagar mulki, gwamnatin jihar Kaduna ta ce ta cika daya daga cikin manyan alkawuran da ta yi wa al'ummar jahar na kammala aikin ruwan na Zaria.

Hukumomi dai sun ce yanzu matsalar ruwa a yankin ta zama tarihi, koda ya ke kashi daya na aikin aka kammala wanda zai bada ruwa ga al'ummar Zaria da Sabon Gari.

Ana saran nan gaba kadan za'a kammala aikin baki daya wanda zai bada damar samar da ruwa ga wasu kananan hukumomi dake yankin.

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El- Rufai ya bukaci al'umma da su rika biyan kudin ruwan Fanfo don samun damar ci gaba da samun ruwan akai-akai.

Wasu al'ummomin yankin sun shaida wa BBC cewa kammala aikin zai taimaka wajen magance matsalolin da suka dade suna fuskanta sakamakon rashin ruwan Fanfo.