British Airways ya dawo da zirga zirgar jiragensa

Dubban fasinjoji sun yi cirko cirko a filayen jiragen sama a sassa daban dabam na duniya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Dubban fasinjoji sun yi cirko cirko a filayen jiragen sama a sassa daban dabam na duniya

Kamfanin jiragen sama na British Airways ya maido da zirga zirgar jiragen sa yau lahadi, bayan wata babbar matsala ta na'urar kwamfuta da katsewar wutar lantarki ta haddasa, ta sukurkuta tsarin zirga-zirgar dubban fasinjoji a sassa daban daban na duniya.

Matsalar dai ta sa kamfani zai biya makuden kudade ga fasinjoji da suka yi cirko cirko a filayen jiragen sama a sassa dabam dabam na duniya.

Wakilin BBC ya ce an soke tashi da saukar jiragen kamfanin daga manyan filayen jirgin sama na London wato filin jirgi na Heathrow da kuma Gatwick saboda cunkoso.

Shugaban kamfanin na BA Alex Cruz, ya musanta zargin da kungiyar ma'akatan sufurin jiragen sama suka yi cewa an samu matsalar ce saboda yadda aka mayar da wasu ma'aikata na sashen fasahar sadarwa zaman kashe wando, da kuma mika ayyukan su ga kasar India.