Ɗan wasan Man United Paul Pogba ya tafi Umarah

Hakkin mallakar hoto Marwan Ahmed
Image caption Paul Pogba ya isa Saudiyya don fara aikin Umarah

Dan wasan kulob din Manchester United Paul Pogba ya tafi kasar Saudiyya don fara aikin Umarah a watan Ramadan, 'yan kwanaki kadan bayan kulob dinsa ya lashe kofin Gasar Europa.

Kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Instagram a ranar Asabar, Pogba ya ce yana kan hanyarsa ta zuwa birnin Makkah domin godewa Allah kan nasarar da suka samu a kakar bana.

Hakazalika, a ranar Lahadi ya wallafa wani bidiyo a shafin wanda yake nuna shi a tsaye a gaban Harami. Kuma sabanin yadda aka saba ganinsa a filin wasa, Pogba ya sauya irin salon askinsa.

Dan wasan wanda da ma Musulmi, ya ce yana yi wa Musulmi barka da azumi.

Rahotannin kafafen yada labarai sun ce Pogba, wanda dan kasar Faransa ne, yana yin ibadarsa ta addinin Musulunci.

Pogba ya koma United a bara daga Juventus a matsayin dan wasan da ya fi kowanne tsada a duniya.

Hakkin mallakar hoto Marwan Ahmed
Image caption Ɗan wasan ya ce yana yi wa Musulmi barka da azumi.
Hakkin mallakar hoto Instagram
Image caption Pogba ne dan wasan da ya fi tsada a duniya
Hakkin mallakar hoto Instagram
Image caption Dan wasan ya wallafa bidiyonsa a shafin Instagram gabanin ya kama hanya zuwa filin jirgin saman garin Manchester ranar Asabar
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Pobga a cikin jirgi a kan hanyarsu ta koma gida bayan lashe Kofin Europa a ranar Laraba