Kalli hotunan Pogba a Ka'aba

Ɗan wasan kulob din Manchester United Paul Pogba ya tafi kasar Saudiyya don fara aikin Umarah kwana kadan bayan lashe kofin Europa.

Pogba

Asalin hoton, Marwan Ahmed

Bayanan hoto,

Ɗan wasan kulob din Manchester United Paul Pogba ya isa Saudiyya don fara aikin Umarah a watan azumin Ramadan

Asalin hoton, Marwan Ahmed

Bayanan hoto,

Pogba shi ne dan wasan da yafi tsada a duniya

Asalin hoton, Marwan Ahmed

Bayanan hoto,

Ɗan wasan wanda da ma Musulmi, ya ce yana yi wa Musulmi barka da azumi.

Asalin hoton, Instagram

Bayanan hoto,

Rahotannin kafafen yada labarai sun ce Pogba, wanda dan kasar Faransa ne, yana yin ibadarsa ta addinin Musulunci.

Asalin hoton, Instagram

Bayanan hoto,

Ɗan wasan ya wallafa bidiyonsa a shafin Instagram gabanin ya kama hanya zuwa filin jirgin saman garin Manchester ranar Asabar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Manchester United ta samu nasara a kan Ajax da ci 2-0 a wasan karshe na Gasar Europa, inda Pobga ya zura kwallo daya, Henrikh Mkhitaryan ya zura guda

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Pobga a cikin jirgi a kan hanyarsu ta koma gida bayan lashe Kofin Europa a ranar Laraba