Amurka na duba yiwuwar hana shiga jirage da laptop

America Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tuni dama Amurkan ta wana fasinjoji daga wasu kasashe shiga jirgi da kwamfutocin laptop

Hukumomi a Amurka suna duba yiwuwar hana mutane shiga da kwamfutocin laptop cikin dukkan jiragen sama masu zirga-zirga tsakanin kasa da kasa, saboda barazanar hare-haren ta'addanci dake kasar ke fuskanta.

Shugaban hukumar tabbatar da tsaron cikin gida ta Amurka, John Kelly, ya ce akwai tabbatacciyar barazanar hare-haren ta'addanci a bangaren jiragen sama na kasar, a don haka, a kwai yiwuwar zai aiwatar da matakin hanin.

Ya ce 'yan ta'adda suna da burin ganin sun kakkabo jirgin sama, musanman ma na Amurka, yayin da yake cikin tafiya a sama.

Dama dai Amurkan ta hana fasinjoji dake tasowa daga wasu kasashe goma, akasarinsu daga Gabas ta Tsakiya, shiga jiragen sama da kwamfutocin na laptop.