Za mu daina dogaro ga Amurka da Burtaniya — Merkel

Angela Merkel a taron G7 Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mrs Merkel ta ce kasashen Turai ba za su cigaba da dogaro da Amurka da Burtaniya ba

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel, ta yi gargadi ƙasashen Turai a kan kada su ci gaba da dogara kacokam a kan Amurka da Burtaniya, bayan zaɓen Trump da kuma fitar Burtaniya daga Tarayyar Turai.

Yayin da take jawabi a wani gangamin yaƙin neman zaɓe, Mrs Merkel ta ce wajibe ne ƙasashen Turai su fuskanci yadda za su gina makomarsu da kashin kansu-- amma za su ci gaba da ƙawance da Amurka da Burtaniya.

Ta ce ta so ƙulla ƙawance mai ƙarfi da ƙasashen biyu har ma da Rasha, amma kuma dole ƙasashen Turai su tashi tsaye da kansu game da makomarsu.

Kalaman nata na zuwa ne bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya ƙi amincewa da shiga yarjejeniyar rage ɗumamar yanayi a taron ƙasashe bakwai masu ƙarfin tattalin arziki G7.

"Yanzu lokaci ya yi da za mu daina dogaro kacokam a kan wasu ƙasashe. Na fahimci wani abu a cikin 'yan kwanakin nan," in ji Mrs Merkel.

A ranar Asabar Mrs Merkel ta bayyana tattaunawa a kan sauyin yanayi a taron G7 ɗin a matsayin maras alkibla.

Stephan Mayer ɗan majalisar dokokin Jamus ne, kuma mai magana da yawun harkokin jami'iyar shugabar gwamnatin Jamus din, ya ce ba sabon abu ba ne cewa Donald Trump mutum ne maras sauƙin kai.

"A bayyane take cewa yana neman ya kai ƙasashen Turai bango. Yana yi mana shiga hanci da ƙudundune" a cewar Mayer.

Shugabannin ƙasashen Burtaniya, da Canada, da Faransa, da Jamus, da Italia da kuma Japan sun nuna goyan bayansu kan yarjejeniyar ɗumamar yanayi ta Paris- amma Shugaba Trump ya ƙi ƙara shigar da Amurka cikin yarjejeniyar.

Mr Trump dai ya ce zai yanke shawara kan batun a cikin mako mai zuwa.

A baya dai ya lashi takobin yin watsi da batun yarjejeniyar Paris ɗin, ya kuma taɓa nuna shakku kan batun ɗumamar yanayin.

Mrs Merkel na kan yaƙin neman zaɓe ne gabanin zaɓukan da za a gudanar a cikin watan Satumba.

Kuri'un jin ra'yoyin jama'a sun nuna alamun cewa za ta sake samu galaba a karo na hudu a matsayinta da shugabar gwamnatin Jamus.

Labarai masu alaka