An tuhumi wadda ta kulle 'ya'yanta a but ɗin mota

Castillo Hakkin mallakar hoto WEBER COUNTY SHERIFF OFFICE
Image caption Uwar yaran, Tori Castillo ka iya fuskantar hukuncin ɗauri a gidan yari ko kuma tara idan aka same ta da laifi

An kama wata mata a Amurka bayan an zarge ta da kulle 'ya'yanta, ɗaya mai shekara biyu da mai shekara biyar a cikin but ɗin mota ta tafi kanti sayayya.

Kafofin yaɗa labarai a Amurka sun ce Tori Castillo 'yar shekara 39, na fuskantar tuhuma kan tozarta 'ya'yan cikinta kuma tuni aka damƙa yaran a hannun mahaifinsu.

Rahotanni sun ce 'yan kallo ne da suka taru suna taraddadi suka yi wa babban yaron mai shekara biyar kwatancen yadda zai buɗe gidan ajiye kayan daga ciki.

Masu wucewa sun lura da yadda motar ke jijjiga, ga kuma hayaniya tana fitowa daga ciki, inda aka ajiye ta a wajen wani kantin sayayya.

Al'amarin ya faru ne ranar Alhamis a yankin Riverdale cikin jihar Utah.

Ba a san ko tsawon sa'a nawa yaran suka shafe a cikin gidan kayan ba.

Jami'in 'yan sandan yankin, Casey Warren ya faɗa wa kafar yaɗa labarai ta KTVX: "Ba daidai ba ne a kulle yaro a cikin mota, ballantana ma gidan ajiye kayan mota.

"Gaskiya matsaloli da dama suna iya aukuwa."

Ya yaba wa mutane "masu kyakkyawar niyya" da suka taimaka wajen fitar da yaran.

A ƙarƙashin dokar jihar Utah, barin yaro ɗan ƙasa da shekara tara a cikin mota ba tare da kulawar wani ba, laifi ne da ake iya hukunta mutum ta hanyar tara ko ɗauri.

An kafa dokar ce a shekara ta 2011 bayan ci gaba da samun mutuwar yaran da ake bari cikin zafi a motoci.

Labarai masu alaka