Waɗanne Amurkawa ne suka mutu don kare musulma?

Taliesin Hakkin mallakar hoto FACEBOOK/AURORA DACHEN
Image caption Mahaifiyar Taliesin Myrddin Namkai-Meche, da ya mutu a lokacin hari ta bayyana ɗanta a matsayin "tauraro mai walwali."

An tara gudunmawar sama da dala dubu 600 ga iyalan Amurkawan da aka far wa lokacin da ƙoƙarin kare wata matashiya musulma da saurayinta a cikin jirgin ƙasa.

An kashe biyu daga cikinsu, Taliesin Myrddin Namkai-Meche da Ricky John Best, yayin da aka ji wa na ukun Micah David-Cole Fletcher mummunan rauni a yankin Portland cikin jihar Oregon ranar Juma'a.

Amurkawan sun shiga tsakani lokacin wani mutum ya far wa matasan -- wadda ɗayansu ke sanye da hijabi -- da kalaman cin mutunci.

Daga bisani an kama mutumin da ake zargi da far wa mutanen, Jeremy Joseph Christian.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan sanda sun fitar da hoton Jeremy Joseph Christian bayan kai farmakin

Nan gaba a ranar Talata ce mutumin ɗan shekara 35 zai bayyana a gaban kotu, don fuskantar tuhuma guda biyu kan mummunan kisan kai da yunƙurin aikata kisan kai da razanarwa da kuma aikata laifin mallakar makamin da aka iyakance amfani da shi.

Hukumar tsaro ta FBI ta ce har yanzu ba ta tabbatar da ko mutumin wanda ake zargin ya furta cewa "a kashe duk musulmai ba" lokacin harin, zai fuskanci tuhume-tuhume kan laifukan nuna ƙyama.

A lokaci guda kuma, Mr Fletcher yana ci gaba da samun sauƙi bayan yankan da aka ji masa a wuya.

Ya wallafa hotonsa daga asibitin da yake kwance tare da wata rubutacciyar waƙa da maryacen ranar Asabar. Wani ɗangon waƙar na cewa: "Na tsokane idon ƙyama kuma na rayu."

An jinjinawa mutanen su uku a matsayin "gwaraza" a yankunansu, tun ma ba Destinee Mangum - matashiya musulma mai shekara 16 da tafiya tare da saurayinta ɗan shekara 17 ba lokacin da aka kai musu hari.

Ta faɗa wa kafar yaɗa labaran KPTV cewa: "Zan so na miƙa godiya ga mutanen da suka sadaukar da rayukansu saboda ni, don kuwa ba su ma san ni ba amma suka mutu saboda ni da saurayina da kuma irin shigarmu."

Kusan mutum dubu ɗaya ne suka taru don tunawa da Mista Namkai-Meche, ɗan shekara 23, wanda ya kammala kwaleji kwanan nana da tsohon soja mai shekara 53 Mista Best, a ranar Asabar.

Labarai masu alaka