Zai kashe kansa don an hana shi takarar shugaban ƙasa a Kenya

Kenya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Hukumar zaben kasar ta hana Peter Gichira takara ne saboda ya gaza samun goyon bayan da ake bukata

Ana tuhumar wani ɗan siyasa a ƙasar Kenya da laifin yunkurin kashe kansa ta hanyar faɗowa daga bene, bayan hukumar zaɓen ƙasar ta hana shi tsayawa takarar shugabancin ƙasar.

Sai dai Mista Peter Gichira ya musanta zargin yayin zaman wata kotu a babban birnin kasar Nairobi, kuma an ba da shi beli.

'Yan sanda sun an kama shi a ranar Asabar yayin da yake kokarin faɗowa daga benen hukumar zaɓen kasar mai hawa shida.

Peter yana daga cikin masu neman takarar shugabancin ƙasar takwas da suka kasa cika sharuddan tsayawa takara a zaɓen da kasar za ta yi a 8 ga watan Agusta mai zuwa.

Peter ba ya cikin 'yan siyasar ƙasar da suka yi fice. An fara saninsa ne bayan yunkurin kashe kansa da ya yi a ƙarshen makon jiya.

An hana shi damar tsayawa a zaben ne bayan da ya gaza samun goyon bayan mutum 2,000 wanda ba su alaka da kowace jam'iyya kuma suka fito daga akalla jihohi 24 cikin 47 da kasar take da su.

Wasu jami'an 'yan sanda biyu ne suka cafke Mister Gichira bayan ya fasa daya daga cikin tagar benen kuma yana kokarin faɗowa, kamar yadda 'yan sanda suka bayyana.

Sai dai ana ganin fafatawar za ta fi zafi ne tsakanin Shugaba Uhuru Kenyatta, wanda yake neman wa'adi na biyu, da kuma jagoran 'yan adawar kasar Raila Odinga, wanda yake takara a karo na hudu.

Labarai masu alaka