Buhari da APC sun jefa Nigeria cikin haɗari — PDP

Fastar Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Hakkin mallakar hoto AFP

Jami'iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta ce shekara biyun da Shugaba Muhammadu Buhari da jami'yyar APC suka shafe a kan mulki ba abin da ya haifar sai ƙuncin rayuwa da jefa ƙasar cikin haɗari.

Ɓangaren Sanata Ahmed Makarfi na PDP, ya ce babu wani abin alfahari a ranar bikin ranar 29 ga watan Mayu - ranar da ƙasar ta koma tafarkin demokuraɗiyya - saboda al'amura sun lalace.

Wata sanarwa da PDP ta fitar ce "gwamnatin APC da Muhammadu Buhari sun lalata tushen demokuraɗiyyar da jam'iyyarmu ta kafa tare da hana 'yan adawa rawar gaban hantsi".

Sai dai muƙaddashin Shugaban Najeriyar Yemi Osinbajo, ya ce sun shafe shekarar 2016 suna ƙoƙarin gyara barnar da PDP ta yi a baya.

A jawabin da ya gabatar domin bikin ranar ta demokuraɗiyya, ya ce gwamnatinsu tana kan hanyar farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar ta hanyar samar da ayyukanci da tsaro da yaƙi da cin hanci da rashawa.

Ya ƙara da cewa ana samun ci gaba a dukkan fannonin gwamnati, sai dai ya amince cewa yaƙi da cin hanci da gwamnatin ke yi na tafiyar hawainiya.

Amma anata ɓangaren PDP, ta ce babu abin da Buhari da APC suka sanya a gaba sai "muzgunawa 'yan adawa da kawar da turakun da suka kafa tsarin demukuraɗiyya".

Ta ƙara da cewa idan aka ci gaba da tafiya a haka, to tana matuƙar tsoron "mummunar makomar da zaɓen shekarar 2019 zai iya haifarwa".

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaba Buhari ya yi wa 'yan Najeriya alƙawura da dama lokacin yaƙin neman zabe

Ra'ayin 'yan Najeriyar dai ya rabu kan rawar da shugaban, wanda yanzu haka ke Ingila domin jinya, ya taka a kan ragar mulki.

Yayin da wasu ke ganin baikonsa tare da alkawarin ba za su sake zabarsa ba, wasu kuwa cewa suke yi shugaban ya taka rawar gani idan aka la'akari da irin matsalolin da ya gada.

Masana na ganin a yanzu da gwamnatin ta cika shekara biyu a kan mulki, hankula za su karkata ne kan harkokin siyasa da yadda za a tunkari zaɓen 2019.

Sai dai rashin lafiyar Shugaba Buhari ka iya kara jefa fagen siyasar kasar cikin ruɗani, ganin cewa babu wanda ya san matsayar shugaban game da zaɓe mai zuwa.

Labarai masu alaka