Bana 'yan gudun hijira za su yi layya a gida — Shettima

Gwamnan jihar Borno Kasheem Shettima
Image caption Za mu mayar da 'yan gudun hijira garuruwansu kwana talatin bayan azumin watan Ramadan

Gwamnatin jihar Borno a Nijeriya ta yi alƙawarin mayar da dubban 'yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya raba da mahallansu zuwa garuruwan da aka sake ginawa nan da wata biyu.

A baya dai gwamnatin Bornon ta yi alƙawarin mayar da waɗannan 'yan gudun hijira garuruwansu kafin ƙarshen watan Mayun wannan shekara.

Gwamnan jihar Kasheem Shettima ya ce jinkirin mayar da mutanen na da alaƙa da buƙatar ƙarasa gine-ginen wasu muhimman wurare kamar makarantu da asibitoci da rijiyoyin burtsatsai kafin mutane su koma garuruwansu.

Wasu alkaluma da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar sun ce mutane fiye da miliyan biyu ne rikicin Boko Haram ya tilastawa barin muhallansu a yankin arewa maso gabashin Nijeriya.

Akasarin waɗannan 'yan gudun hijira na zaune ne a sansanoni daban-daban a faɗin yankin, ko da yake, mafi yawan sansanonin na cikin Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Baya ga haka akwai 'yan gudun hijrar Nijeriya sama da dubu 450 da ke zaune a wasu sansanonin da ke ƙasashen Nijar da Kamaru da Chadi da suka nemi mafaka sakamakon hare-haren Boko Haram.

"A garin Damasak kaɗai akwai mutum dubu 72, kuma mun gina garin har zuwa kashi saba'in da biyar cikin ɗari. Inda muka samu matsalaloli su ne garuruwan Bama da Gwoza ko da yake, an ci karfin aikin."

Duk da yake, har yanzu akwai matsalolin tsaro a wasu yankuna da ke dajin kusa da garin Bama, amma gwamna Shettima ya bayar da tabbacin cewa wannan ba zai hana mayar da mutane garuruwansu ba.

Hakkin mallakar hoto Borno state government
Image caption Gwamnatin jihar Borno na kan aikin gina garuruwan 'yan gudun hijrar Boko Haram

Ya ce gwamnati za ta dauki matakan da duk suka dace na ganin ta kare rayukan mutane da dukiyoyinsu.

"Na bayar da tabbacin cewa kwana talatin bayan azumi za mu mayar da su, mun yi imani mutane za su yi sallar layya a garuruwansu."

Ƙauyukan da ke bayan Dutsen garin Gwoza in ji gwamna Shettima, na daga cikin wuraren da har yanzu ba zai yiwu a mayar da mutane ba, saboda ɓurɓushin 'yan Boko Haram da ke maƙale a can, ko da yake ya ce sojoji na ci gaba da ƙoƙarin kakkaɓe su.

Ya kuma ce 'Yan gudun hijirar Nijeriya dubu saba'in da takwas ne a kasar Kamaru. Kuma akwai wasu dubu bakwai a garin Banki da ke kan iyakar Nijeriya da Jamhuriyar Kamaru, yayin da wasu ke ƙauyen Pulka na garin Gwoza."

Gwamna Shettiman ya ce za a mayar da makarantar sakandaren garin Bama matsugunan waɗannan 'yan gudun hijira da zarar an kwaso su, kafin a san matakan da za a ɗauka na tallafa musu da sake mayar da su wurarensu na asali.

Jihar Borno dai nan ce inda hare-haren mayaƙan Boko Haram suka fi muni, don kuwa ita ce tungar Boko Haram kafin sojin Nijeriya su fatattaki mayaƙanta.

Labarai masu alaka