Guguwa ta sa kwashe mutum miliyan 1 a Bangladesh

Kasar Bangladesh Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dubban mutane ne aka kwashe zuwa tudun mun tsira a Bangladesh

Wata gawurtacciyar guguwa ta auka wa gaɓar tekun Bangladesh, cikin rakiyar mamakon ruwan sama da ƙaƙƙarfar iska mai gudun da ya zarce kilomita 100 cikin sa'a guda.

Guguwar mai suna Mora ta dira ne a wani yanki tsakanin birnin Chittagong da gaɓar tekun Cox's Bazar mai harkokin kamun kifi.

Hukumomi na kwashe sama da mutum miliyan ɗaya zuwa wasu yankuna da ba sa fuskantar hatsari.

Hukumomi sun umarci birane masu tashoshin jiragen ruwa a kudu maso gabashin Bangladesh su kasance cikin shirin ko-ta-kwana.

Gawurtacciyar guguwar ta taso ne bayan wani mamakon ruwan sama da aka tafka a ƙasar Sri Lanka, da ta haddasa ambaliya da zaftarewar ƙasar da ya hallaka aƙalla mutum 180.

Ambaliyar ruwa mafi muni da aka taɓa yi cikin shekara 14 a tsibirin ta shafi mutane fiye da rabin miliyan. Haka kuma, mutane fiye da 100i sun yi ɓatan dabo.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Ana ta kwashe kaya daga kantuna a bakin tekun Patenga a birninChittagong

Mutane a gundumar Chittagong sun cunkusu a matsugunai kimanin 500 na tudun mun tsira, bayan da aka sanar da gargadin ta amsa-kuwwa.

An yi amfani da gine-ginen makarantu da ofisoshin gwamnati wajen tsugunnar da mutane, kuma an umarci mazauna yankunan da ke kan tsaunuka su ƙaurace.

Wani wakilin BBC ya ce Duk da cewa Bangladesh ta saba da fuskantar gawurtattun guguwa, mutane da dama ba sa zama a ingantattun wuraren da za su rika jurewa yanayi maras kyau.

Don haka rayuwarsu, da amfanin gonarsu da suka dogara da su kan fuskanci barazana a duk lokacin da irin guguwa ta auka.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ambaliyar ruwa a kasar Sri Lanka ta raba mutane fiye da rabin miliyan da matsugunansu

Bangladesh ba ta gama murmurewa daga bala'in ambaliyar ruwan da ya auka mata a yankin arewa maso gabashin kasar ba cikin watan Afrilu, wadda ta lalata gonakin shinkafa, tare da haddasa ƙazamin tashin farashinta a kasuwanni.

Haka kuma gaguwar na iya shafar wasu yankunan arewa maso gabashin Indiya da yammacin ƙasar Myanmar.

Kusurwar tekun Bengal na ɗaya daga cikin gaɓar teku mafi fuskantar baƙin hadari a duniya.

Labarai masu alaka