Damusa ta kashe mai kula da namun daji

Tigers Hakkin mallakar hoto Hamerton zoo
Image caption Gandun namun dajin na da kewayen damusoshin ƙasar Malaysia da Bangladesh

Wata mai kula da namun daji, Rosa King ta mutu "sakamakon tsurewa" bayan wata damusa ta shiga wani kewaye da take ciki a wani gandun namun daji.

Matar mai shekara 33, ta mutu ne a gandun namun dajin Hamerton, da ke kusa da Huntingdon, a yankin Cambridgeshire a Ingila.

'Yan sandan Cambridgeshire sun ce: "Wata damusa ce ta ɓalle inda ta shiga wani kewaye da ita mai kula da namun dajin ke ciki. Kuma abin ya zo da ƙarar kwana, matar ta mutu a wajen."

An fitar da masu ziyara daga gandun namun daji. Kuma 'yan sanda sun ce babu lokacin da dabbar ta kuɓuce daga cikin kewayen.

Gandun namun dajin Hamerton ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa: "Wannan (mutuwa) ga alama ta auku ne sakamakon tsananin tsurewa da mai kula da dabbobin ta yi.

"Muna matuƙar juyayi da taya abokan aiki da 'yan'uwa da abokai alhinin wannan mummunan al'amari."

Hakkin mallakar hoto HAMERTON
Image caption A bara ma sai da aka ƙara buɗe wani kewayen ajiye damusa a gandun

Gandun namun dajin ya ce za a gudanar da bincike kan wannan al'amari.

Wani mai ziyara a gandun namun dajin ya ce: "Mun kusa zuwa kewayen damusar sai wani mai kula da namun dajin ya ƙwalla mana kira cewa duk mu yi sauri mu fita."

Gandun namun dajin wanda aka buɗe a shekarar 1990 na ƙunshe da damusoshin ƙasar Malaysia da na Bangladesh da kyarkeci da dila da sauran dabbobi da nau'o'in tsuntsaye.

Ko a shekara ta 2008 ma wani yaro ɗan shekara tara ya gano wata damusa a lambun gidansu bayan ta kuɓuce daga dandalin.

Labarai masu alaka