Igbo sun tsayar da al'amura don goyon bayan Biafra

Biafra
Image caption Manyan kasuwanni sun kasance a rufe

Rahotanni daga Kudu maso Gabashin Najeriya na cewa al'amura sun tsaya cak a wasu manyan biranen yankin don nuna hadin kai kan kiran da kungiyoyin da ke fafutukar kafa yankin Biafra suka yi na kasancewa a gida.

Kungiyoyin IPOB da MASSOB sun yi wannan kira ne na cewa mutane su zauna a giadajensu a matsayin zanga-zangar lumana, don tunawa da shekara 50 na fara fafutukar kafa yankin Biafra da marigayi Chukwuemeka Ojukwu ya yi.

Wakilin BBC da ke Enugu AbudsSalam Ibrahim Ahmed ya ce fiye da kashi 90 cikin 100 na shagunan da ke birnin a rufe suke, haka ma babbar kasuwar birnin ta kasance a rufe.

Sai dai kuma ana ci gaba da harkokin sufuri.

Image caption Masu fafutukar kafa yankin Biafra sun sha yin zanga-zanga

Haka ma a birnin Umuahia inda nan ne garin jagoran masu fafutuka na kungiyar IPOB Nmandi Kanu ya fito, yawanci shaguna sun kasnace a rufe amma akwai kadan da suka bude.

A birnin Anacha na jihar Anambra kuwa, harkokin da suka hada da na kasuwanci da sufuri da makarantu da bankuna duk sun kasance a rufe.

Dukkan sauran jihohin yankin ma ana cikin irin wannan yanayi. Yankin Kudu maso Gabas dai ya kunshi jihohin Anambra da Enugu da Abia da Imo da kuma Ebonyi.

Zuwa yanzu dai babu wani rahoto na tashin hankali, amma tuni aka jibge jami'an tsaro a muhimman wurare da ke jihohin yankin.

Labarai masu alaka