Hotunan abubuwan tarihin da suka faru a Afirka a makon jiya

Hotunan makon jiya mafi kayatarwa daga sassa daban-daban na Afirka da duniya.

Wata 'yar sandar Najeriya tana fareti a ranar bikin Demokuradiyya ta kasar a birnin Owerri a ranar 29 ga watan Mayu, 2017.

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Wata 'yar sandar Najeriya tana fareti a ranar bikin Demokuradiyya - ranar da kasar ke bikin kawo karshen mulkin soja a shekarar 1999.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

'Yar Najeriya Olufunke Oshonaike tana fafatawa a zagayen farko na gasar kwallon tebur na duniya a kasar Jamus a ranar Laraba.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Ranar Talata - Emmanuel Rutema dan kasar Tanzaniya na sa sabon hannun roba bayan da wani wanda yake neman hannun zabiya ya datse nasa hannun domin amfani da shi wajen yin magani.

Asalin hoton, Michael Khateli

Bayanan hoto,

Sabuwar tashar jirgin kasa ta birnin Mombasa wacce aka bude ranar Laraba a lokacin bikin kaddamar da sabon layin jirgin da kasar China ta gina.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Ranar Asabar shugaban Kenya Uhuru Kenyatta da Shugaban Guinea Alpha Conde da Shugaban Bankin Raya Afirka Akinwumi Adesina, da mukaddashin Shugaban kasar Najeriya Yemi Osinbajo da Firayi Ministan Habasha Hailemariam Desalegn sun dauki hoto da Shugaban Amurka Donald Trump a wajen taron koli na kungiyar kasashen G7

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Mista Trump na da masoya a kudu maso gabashin Najeriya, inda a ranar Talata wasu suka yi bikin shekaru 50 da shelar kafa kasar Biyafara. Shelar ta jawo yakin basasan da ya yi sanadiyar halaka mutane miliyan daya...

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Wadannan yaran a birnin Abidjan na kasar Cote d'Ivoire na kallon hotunan yakin basasar kasar ne

Asalin hoton, AFP/PGDBA ^ HND

Bayanan hoto,

'Yan matan Chibok da aka ceto daga hannun kungiyar Boko Haram sun fara samun kulawa ta musamman a Abuja

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Salif Sylla na kasar Guinea ya fadi a lokacin wasansu da Argentina a gasar cin kofin kwallon kafa na matasa 'yan kasa da shekara 20 a Koriya ta Kudu

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Wani magini yana aiki a birnin Harare na kasar Zimbabwe ranar 26 ga watan Mayu 2017

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

A ranar Litinin kungiyar mawaka mai farin jini ta Ivory Coast wato Magic System sun kai wata ziyara zuwa wata makaranta dake da suna iri daya da ta kungiyarsu a birnin Abidjan

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Mambobin kungiyar wasannin gargajiya na kasar Kongo sun gabatar da rawan taken Kongo a Bhopal na kasar Indiya ranar Laraba