'Yan Najeriya na ƙorafi kan ƙarin kuɗin Hajjin bana?

Kaaba, Makkah, Saudi Arabia Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Maniyyata aikin hajji zasu biya fiye da Naira miliyan daya da rabi a bana

Maniyyata aikin hajji daga Najeriya za su biya fiye da Naira 1,500,000 kafin su sami sauke farali a bana.

Zuwa yanzu, hukumar kula da ayyukan Hajji ta Najeriya ta fitar da farashin da ko wanne maniyyaci daga jihohi 22 cikin 36 na kasar zai biya.

Mafi kankantar farashin shi ne na Naira 1,480,000 da maniyyatan jihar Katsina za su biya. Maniyyatan jihar Oyo sune zasu biya farashi mafi yawa na Naira 1,584,069.

Bashir Abubakar El-nafaty mazaunin Abuja kuma maniyyaci ne a bana ya koka da yadda aka sami karin farashin aikin hajjin na bana.

"A gaskiya farashin nan da aka fitar bai yi mana dadi ba", in ji Bashir. "Wannan karin kudin ba kadan ba ne, kuma ya bata wa maniyyata lissafinsu."

Mallam Bashir ya shafe shekara guda yana ajiyar kudaden aikin hajjin.

"Kafin karin dai na ajiye naira miliyan daya, sai kwatsam muka ji an kara Naira 500,000. A da muna fatan karin da za mu yi ba shi da yawa", in ji shi.

A bara dai maniyyata daga arewacin kasar sun biya Naira 998,248.92 a karamar kujera, wasu kuma sun biya Naira 1,047,498.92 na matsakaiciyar kujera, kana masu babbar kujera sun biya Naira 1,145,998.92.

Su kuma maniyyata daga kudancin kasar sun biya Naira 1,008,197.42, su kuma masu matsaikaiciyyar kujera kuma sun biya N1,057,447.42, inda masu babbar kujera suka biya Naira 1,155,947.42.

A bana an soke wannan tsarin kujeru daki-daki, inda aka mayar da shi na bai daya, kuma kowane maniyyaci zai biya abin da jiharsa ta kayyade.

A bana an tsayar da guzurin bai daya na dala 800 na Amurka.

A nata bangaren, hukumar jin dadin maniyyata ta Najeriya ta kare ƙarin da cewa tashin farashin kuɗin musaya da alhazan ke buƙata ne ya haddasa shi.

Ga jaddwalin kudaden da maniyyata daga Najeriya za su biya:

 • Nasarawa:1,544,894.16
 • Niger:1,525,483.30
 • Kaduna:1,535,503.68
 • Kano:1,537,859.97
 • Katsina: 1,498,502.70
 • Adamawa:1,530,101.18
 • Yobe:1,520,101.18
 • Kano:1,537,859.97
 • FCT:1,538,218.62
 • Bauchi:1,523,122.41
 • Plateau:1,529,036.80
 • Zamfara:1,510,461.65
 • Sokoto:1,524,618.90
 • Gombe:1,516,118.90
 • Benue:1,522,118.90
 • Kebbi:1,534,659.85
 • Taraba:1,521,138.21
 • Osun:1,548,153.42
 • Armed Forces:1,538,379.22
 • Ogun:1,561,943.97
 • Anambra:1,511,173.77
 • Kwara:1,501,571.27
 • Ekiti:1,525,191.27
 • Edo:1,551,331.87.
 • Oyo:1,584,069.02.

Ban da wadannan kudaden, akwai Naira 38,000 na hadaya da kowane maniyyaci zai biya daga aljihunsa a Makkah.

Bashir Abubakar ya ce yawancin maniyyata ba za su iya biyan karin kudin ba.

"Ni ma kaina da nake magana, idan ban samu karin ba, gaskiya hakura zan yi. Na tabbata kashi 50 cikin dari na wadanda suka yi niyyar zuwa wannan aikin hajjin ba za su sami damar zuwa ba saboda karin yayi yawa."

Labarai masu alaka