An dakatar da ɗan wasan da ya sumbaci 'yar jarida

Dan wasan Tennis na Faransa Maxime Hamou Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Lamarin ya faru ne bayan da Pablo Cuevasda na kasar Uruguay ya fitar da Hamou a zagayen farko na gasar a ranar Litinin.

Wani ɗan wasan kwallon Tennis na Faransa ya fuskanci dakatarwa saboda sumbatar wata 'yar jarida sau da dama a lokacin da take hira da shi kai tsaye ta gidan Talbijin.

Jami'an shirya gasar manyan wasannin kwallon Tennis na 'French Open' ne suka dauki wannan mataki a kan Maxime Hamou .

Ɗan wasan mai shekara 21, ya sumbaci 'yar jaridar Maly Thomas bayan ya kamo wuyanta, duk da ƙoƙarin kufcewa da ta yi.

Hukumar wasan kwallon Tennis ta kasar Faransar (FTT) ta yi tir da abin da ta kira "mummunar dabi'a", ta kuma buƙaci a gudanar da bincike.

Lamarin ya faru ne bayan an fitar da shi daga wasannin zagayen farko na gasar a ranar Litinin.

Wannan shi ne al'amari na baya-bayan nan da ya haifar da zarge-zargen cin zarafin mata masu aiko da rahotannin wasanni.

Lamarin dai ya fusata masu mu'amala da shafukan sada zumunta ciki har da Cécile Duflot wata 'yar siyasa a Faransa.

"Ya sumbace ta ta karfin tsiya, ta yi ƙoƙarin kufcewa, ya riƙo wuyanta kuma kowa yana ta...dariya," kamar yadda ta wallafa a shafinta na Twitter.

Wata jaridar ƙasar Faransa Huffington Post ta ambato Ms Maly Thomas na bayyana halayyar ɗan wasan a matsayin "rashin kan gado".

"Da ba don an hasko mu kai tsaye a talbijin ba, da na kai masa naushi, in ji ta.

Hakkin mallakar hoto EUROSPORT
Image caption Hamou ya yi ta maimaita sumbatar 'yar jaridar a lokacin hirar kai tsaye

Dan wasan dai, Hamou ya nemi afuwa kan abin da ya aikata.

A wata sanarwa a shafin sada zumunta na Facebook a ranar Talata, Hamou ya ce: "Ina matuƙar neman gafara ga Maly Thomas, idan ranta ya ɓaci, ko ta kaɗu game da halayyata a lokacin hirarmu.

"Har yanzu a kullum ina ƙara koyon darasi daga kura-kuraina don zama ɗan wasa na gari, kuma mutumin kirki."

Gidan talbijin na Eurosport ya yi lale marhabin da matakin ɗan wasan na neman gafara, tare da isar da batun ga masu kallo da mai yiwuwa ba su ji daɗin abin da suka gani ba.

"Muna matuƙar nuna nadamarmu kan abin da ya faru lokacin hirar da muka watsa a jiya," in ji Eurosport a wata sanarwa.

"Halayyar wanda ake hira da shi ɗin sam ba ta dace ba, kuma ba za mu taɓa yarda da irin wannan abu ta kowanne hali ba."

Labarai masu alaka