An kai samame kan masu jabun ruwan zamzam a Saudiyya

Ruwan Zamzam Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Hukumomin Saudia sun gargadi jama'a da su yi hattara game da jabun ruwan Zamzam

Hukumar kula da ingancin abinci ta Saudiyya ta ce ta lalata dubban kwalaben ruwan zamzam na jabu sannan kuma ta rufe wasu gidajen da ake yin ruwan a wani samame da ta kai a fadin kasar.

Jaridar Saudi Gazette wadda ta rawaito labarin ta ce mutane na yin ruwan na jabu ne saboda tsananin bukatar zamzam da jama'a ke da ita musammam don yin buɗa-baki a wannan wata na Ramadan.

Hukumar ta gargaɗi mutane su kula kada su faɗa tarkon masu yin jabun zamzam.

Wannan lamari dai na jabun ruwan zamzam ya haifar da damuwa ga hukumomin kasar ta Saudi Arabia.

Baya ga 'yan kasa, mahajjata daga kasashen daban-daban kan sayi ruwan zamzam din da dama su kai gida.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mahajjata daga kasashen daban-daban kan sayi ruwan zamzam din da dama su kai gida

Don taka birki ga 'yan kasuwar jabun, tare da tabbatar da mutane sun samu ingantaccen ruwan zamzam, gwamnati ta yi wa wasu zababbun kantuna rajistar sayar da ruwan mai daraja.

Duk da haka, hukumomi sun ce an samu wasu kantunan da ba a amince da su ba na yin kafar-ungulu wajen yi wa ruwan zamzam din algus da na famfo.

A wani samame a baya-bayan nan, hukumomi a birnin Madinah sun ƙwace kwalabe fiye da 3,000 na zamzam ɗin da aka yi masa gauraye.

An kuma manna takardu masu tambarin kamfanin ruwan zamzam na Sarki Abdalla, a wani wurin ajiyar motoci a wata unguwa.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mutane na yin jabun zamzam din saboda tsananin bukatarsa da jama'a ke yi don buda-baki a wannan wata na Ramadan.

Har ila yau, ma'aikatar ciniki da zuba jari ta Saudiyar ta sanar da rufe wata masana'anta a yankin Buraidah, kan samunta da ɗura ruwan famfo a kwalaben zamzam.

Sun kuma gano kwalabe 6,500 na jabun zamzam.

Ma'aikatar ta kuma rufe wani wurin ajiyar kaya da ta gano a birnin Makka, inda ake ajiye ruwan ana sayar wa shaguna. An kuma lalata kwalabe dubu dari biyu.

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Saudiyyar ta gargadi jama'a su guji sayen ruwan zamzam a kantunan da ba su da rijista.

Labarai masu alaka