United ta fi kowacce ƙungiya arziƙi a bana

Man United Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Manchester United ce ta lashe gasar Europa ta bana

Manchester United ita ce ƙungiyar ƙwallon ƙafa mafi arziƙi a illahirin Turai, inda darajarta ta kai kimanin fam biliyan 2.6 a cewar wata cibiyar harkokin kasuwanci KPMG.

Zakarun gasar Europa League ɗin sun shiga sahun gaba na ƙididdigar cibiyar inda ta sha gaban gaggan ƙungiyoyin Spaniya, Real Madrid da Barcelona.

Nazarin ya bibiyi haƙƙoƙin yaɗa wasannin ƙungiya, da yiwuwar kawo ribarta da shahara da damammakin buga wasanni da mallakar filin wasa.

Nazarin wanda ya ƙunshi ƙungiya 32, kulob-kulob ɗin Ingila sun yi mamaya, inda suka kankane matsayi shida a cikin gurbi guda goma na sama.

Shugaban harkokin wasanni a cibiyar KPMG kuma mawallafin rahoton, Andrea Sartori ya ce ɗaukacin darajar harkar wasannin ƙwallon ƙafa ta bunƙsa a shekarar da ta gabata.

A cewarsa: "A lokaci guda wannan ya bayyana wani ɓangare na bunƙasar yaɗa wasannin ƙwallon ƙafa da faɗaɗa harkokin kasuwancin kulob-kulob a faɗin duniya, da jarin da suke zubawa don mallakar kadarori na ƙashin kai, da na zamani, bugu da ƙari kuma tsare-tsaren gudanarwa masu ɗorewa na daga cikin manyan dalilan da suka janyo wannan bunƙasa."

"Ta fuskar darajar haƙƙin yaɗa harkokin wasanni, Gasar Firimiyar Ingila ta yi wa sauran takwarorinta na Turai zarra, ko da yake su ma sauran manyan gasannin ƙasashe sun fito da fayyatattun tsare-tsare don yin gogayya wajen samun magoya baya a faɗin duniya."

Manyan ƙungiyoyin Turai guda 10 ta fuskar 'darajar harkokin cinikayya'

Manchester United -3.09bn euros

Real Madrid - 2.97bn euros

Barcelona - 2.76bn euros

Bayern Munich - 2.44bn euros

Manchester City - 1.97bn euros

Arsenal - 1.95bn euros

Chelsea - 1.59bn euros

Liverpool - 1.33bn euros

Juventus - 1.21bn euros

Tottenham - 1.01bn euros

Majiya: KPMG

Sai dai Mista Sartori ya ce ƙungiyoyin sun gaza yin tasiri a ɗaiɗaikunsu wajen bunƙasa kuɗin shiga ta fuskar yaɗa wasanni.

A bana, darajar ƙungiyoyin Turai 10 ta ƙaru da fiye da yuro biliyan ɗaya, ninki biyu idan an kwatanta da shekarar 2016.

Tottenham Hotspur da Juventus ta Italiya ne sabbin shiga rukunin hamshaƙan ƙungiyoyin Turai, inda Tottenham ta jeho Paris Saint-Germain ta Faransa daga matsayi na goma.

Duk da mamayar da ƙungiyoyin Firimiya suka yi, Spaniya ce ƙasa guda ɗaya da ke da ƙungiya biyu da rahotanni suka ce na da "darajar harkokin kasuwanci" ta fiye da yuro biliyan biyu, Real Madrid da Barcelona.

Labarai masu alaka