An ɗaure Malamin addini saboda ɓata wa ɗan fim suna

A watan Maris din 2017 ne aka yi wani bikin baje kolin fina finai a birnin Dammam
Image caption A watan Maris din 2017 ne aka yi wani bikin baje kolin fina finai a birnin Dammam

An yanke wa wani Malamin addinin Musulunci hukuncin ɗauri a kasar Saudiyya, saboda ya ɓata wa wani sanannen jarumin fim suna.

An yankewa Saeed bin Farwa hukuncin zaman kwana 45 a gidan yari, saboda ya kira Nasser al-Qasabi a matsayin "kafiri".

Malamai sun gudanar da wani gangami a kan Mista al-Qasabi don mayar da martani ga wata shahararriyar gidan talabijin inda jarumin kuma mai barkwanci ke yin ba'a ga kaifin kishin Islama.

Mista al-Qasabi ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa, wannan ya nuna cewa ba wanda ya fi karfin hukunci.

Labarai masu alaka