An yi artabu tsakanin 'yan sanda da sojoji a Calabar

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta wallafa barnar da aka yi mata a shafinta na Facebook Hakkin mallakar hoto Nigeria Police
Image caption Rundunar 'yan sandan Najeriya ta wallafa barnar da aka yi mata a shafinta na Facebook

Rahotanni daga birnin Calabar na jihar Cross River da ke Kudancin Najeriya na cewa an tafka wani fada tsakanin 'yn sanda da sojojin ruwan Najeriya, inda ake tunanun an yi asarar rayuka da wasu da dama kuma sun jikkata.

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta tabbatarwa BBC faruwar lamarin, inda ta har ta wallafa hotunan barnar da ta ce sojojin sun yi a ofishin 'yan sandan.

Amma rundunar ba ta yi karin bayani kan asarar rayuka ko jikkata ba.

Lamarin ya faru ne ----bayan wata sa'insa da ta kaure tsakanin jami'an 'yan sanda--- da na sojojin ruwan.

Wasu rahotanni sun ce rikicin ya fara ne a yayin da wani dan sanda ya yi kokarin tsayar da motar sojojin, wadda ta ki bin umarnin danjar bayar da hannu.

Fadan ya yi kamari ne yayin da wasu manyan jami'ai suka yi kokarin sasantawa, amma daga bisani sai al'amura suka rincabe.

Kafar yada labarai ta Premium Times ta ruwaito cewa wani ganau ya shaida mata cewa daga nan sai sojojin suka shiga cikin ofishin 'yan sandan na Akim inda suka fara harbe-harbe suka kuma kona ofishin.

Labarai masu alaka