Priyanka Chopra na shan suka kan bude cinyoyinta gaban Firai Minista

Chopra posted this picture on Facebook Hakkin mallakar hoto Priyanka Chopra
Image caption Misis Chopra ta wallafa wannan hoton a shafin Facebook

Wasu masu amfani da shafukan sada zumunta na zamani na yin suka ga jaruma Priyanka Chopra a kan kayan da ta saka da yake bayyana cinyoyinta a wata ganawa da ta yi da Firai Ministan Indiya Narendra Modi.

Wasu masu amfani da shafukan Facebook sun shaida mata cewa hakan nuna rashin girmamawa ne ga Firai Ministan.

Jarumar ba ta nuna nadamar yin hakan ba, inda ta saka wani hotonta tare da mahaifiyarta sanye da guntuwar riga, mai taken, "legs for the day," wato "kafafun wannan rana.

Dama dai wasu taurarin fina-finan Indiyan ma na fuskantar suka daga wajen jama'a kan yanayin sa tufafinsu.

A shekarar 2014 ma, wata jarida a Indiya ta bayyana Deepika Padukone ta saka wani hotonta inda ake iya ganin mamanta a shafinta na Tweeter.

Padukone ta yi wa jaridar martani a shafinta na Tweeter. inda ta ce, "Eh! Ni mace ce, ina da mama! Ko akwai matsala ne?" Kuma jarumai da dama sun fito sun nuna mata goyon bayansu.

An fara ce-ce-kucen a kan Priyanka Chopra ne, bayan da wani gidan talbijin ya sanya wani hotonta tare da Mista Modi, tana mika masa godiyarta, a kan ganawar da ya yi da ita a Berlin na kasar Jamus, "Duk da yawan ayyukansa amma ya sadaukar da lokacinsa," in ji Priyanka.

Ko da yake ba a dauki lokaci mai tsawo ba, kafin shigar tata ta zama wani batu da ake ce-ce-kuce a a kansa, inda mutane da yawa ke sharhi cewa hakan da ta yi cin mutunci ne ga Mista Modi suna da kuma magoya bayansa.

Ga wasu daga cikin masu sukar a shafukan sa da zumunta:

Hakkin mallakar hoto Avani Borkar
Hakkin mallakar hoto Shirish
Hakkin mallakar hoto Raviteja Reddy

Da farko dai kamar Misis Chopra ba ta yi niyyar mayar wa mutane martani ba, sai dai daga baya ta shammace su a shafinta na Instagram inda har ta sanya hotonta da na mahaifiyarta, kuma tabbas kafarta a bude take.

A kasa da sa'a hudu, an samu sama da mutum 100,000 da suka nuna sha'awarsu ga hoton.

Hakkin mallakar hoto Priyanka Chopra
Hakkin mallakar hoto Raj Singh
Hakkin mallakar hoto Priyanka Bhaduri

Labarai masu alaka