Tsohon shugaban kasa zai tsaya takarar Majalisar Dokoki

Abdoulaye Wade Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Abdoulaye Wade ya yi watsi da kiran da aka yi masa na ya sauka daga mulki

Tsohon shugaban kasar Senegal Abdoulaye Wade, zai tsaya takara majalisar wakilan kasar.

Mista Wade mai shekara 91 zai tsaya takarar ne a zabukan da za a yi a watan Yuli mai zuwa.

Zai tsaya takarar ne a jam'iyyar adawa ta PDS.

Mista Wade ya shugabanci kasar ta Senegal daga shekarar 2000 zuwa 2012. Ya kuma sha kaye a hannun shugaba mai ci yanzu Macky Sall, a zaben 2012.

Senegal dai kasa ce a yankin yammacin Afirka.

Labarai masu alaka