An ƙaddamar da layin dogo da zai ratsa ƙasashen gabashin Afirka

Layin dogo Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption China ce ta gina layin dogon

Kasar Kenya ta kaddamar da sabon layin layin dogo da zai hade birnin Mombasa da babban birnin kasar Nairobi, cikin watan 18.

Shugaba Uhuru Kenyatta ya ce layin dogon wanda ya lamushe kudi dala biliyan 3.2 da aka ciwo bashinsu daga kasar China, zai bude sabon shafi ga kasar.

Ya yi gargadin cewa zai dauki matakin dakile masu barnatar da dukiyar gwamnati, bayan da aka kama mutum hudu da laifin lalata wani bangare na hanyar.

Shirin dai shi ne babban ci gaba da kasar ta samu tun samun 'yancin kai.

Image caption Sabon layin dogon zai hade daukacin kasashen gabashin Afirka

Layin dogon mai nisan kilomita 470 a na sa ran zai hade kasashen kudancin Sudan da kuma gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, da Rwanda, da Burundi da kuma Ethiopia zuwa tekun Indiya.

A makon da ya gabata ne, Mista Kenyatta ya samo karin kudi dala biliyan 3.6 domin fadada layin dogon mai nisan kilomita 250 yamma daga tsakiyar garin Naivasha zuwa Kisumu.

Sai dai aikin na fuskantar suka daga masu adawa, wanda suka ce ya yi tsada matuka, kuma zai kawo wa tattalin arzikin kasar nakasu

Gwamnatin ta ce tana bukatar inganta harkar sufuri saboda jan hankalin masu zuba jari daga kasashen waje.

Mista kenyatta, wanda ke ganin ci gaban a matsayin wata dama da zai yi amfani da ita wajen sake tsayawa takara a zaben watan Agusta, ya ce Layin dogon wani sabon sauyi ne a tarihin kasar.

"Tarihin wannan aiki ya fara ne shekara 122 da suka shude, lokacin da da Birtaniya, kasar da ta yi wa Kenyan Mulkin mallaka ta fara aza harsashin aikin, inda tun daga wancan lokacin ba a samu wani karin ci gaba ba."

"A yau duk da cewa muna shan suka, a yau muna bikin bude 'Madaraka'(Sunan ranar da Kenya ta samu 'yancin kai) wanda zai fara sauya tarihin Kenya a shekaru 100 masu zuwa," in ji Shugaba Kenyatta.

Labarai masu alaka