Harin bam ya kashe ma'aikacin BBC da wasu mutum 80

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Yawanci fararen hula ne suka mutu a harin

A kalla mutum 80 ne suka mutu ciki har da wani ma'aikacin BBC yayin da wata mota ta tayar da bam a yankin da ofisoshin jakadancin kasashen waje suke a Kabul babban birnin Afghanistan.

An kai harin ne kusa da dandalin Zanbaq inda yake da matsanancin tsaro, kuma mutum 350 ne suka jikkata yawancin su fararen hula.

Fashewar bam din -- wanda aya faru da safiyar Laraba ya yi tsananin karfin da sai da ya sa tagogi da kofofin gine-ginen da ke da nisan daruruwan mitoci suka farfashe.

Kungiyar Taliban da ke yawan kai hare-hare birnin ta ce ba ita ta kai harin na yau ba. Sai dai har yanzu ba a ji ta bakin kungiyar IS ba da ita ma take kai hare-hare.

Dukkan kungiyoyi biyu dai sun musanta cewa su suka kai hare-hare na baya-bayan nan kasar.

BBC ta tannatar da mutuwar wani direbanta da ke aiki a Afghanistan Mohammed Nazir.

A ina harin ya faru?

Bam din ya tashi ne da misalin karfe 8.25 na safe a lokacin da zirga-zirga ta fi yawa a yankin da ofisoshin da jakadancin kasashen waje suke.

Motar daukar marasa lafiya ta dauki wadanda suka jikkata a harin, yayin da 'yan uwan wadanda lamarin ya ritsa da su suka taru a inda lamarin ya faru, da kuma asibitocin domin gano 'yan uwansu.

Hotuna sun nuna yadda gomman motoci suka kone. Inda sama da motoci 50 suka lalace.

Mai magana da yawun 'yan sandan Kabul Basir Mujahid, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa bam din ya fashe ne a kusa da ofishin jakadancin Jamus, sai dai ya kara da cewa "Abu ne mawuyaci a gano inda maharan suka yi niyyar kai harin."

Akwai manya-manyan gine-gine a yankin da harin ya faru, wadanda suka hada da fadar shugaban kasa, da kuma ofisoshin jakadancin kasashen waje, ciki har da na Burtaniya.

Rahotonni sun ce bam din ya tashi ne a cikin wata babbar mota ta daukar ruwa.

Wakilin BBC a Kabul Harun Najafizada ya ce an yi ta tambaya game da yadda motar ta tarwatse a yankin da ke da matukar tsaro.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Motocin daukar marasa lafiya sun yi ta daukar mutenen da suka jikkata

Da farko dai rahotonni sun ce fararen hula ne suka fi jikkata a lamarin.

Ma'aikatar Lafiyar kasar ta ce ana sa ran yawan wadanda suka jikkata na iya karuwa.

Mai magana da yawun ma'aikatar Ismael Kawoosi, ya ce: "Har yanzu ana kawo gawarwaki tare da marasa lafiya asibitoci."

Ma'aikatar cikin gidan kasar ta yi kira ga mazauna kasar da su bayar da gudunmowar jini, yana mai cewa "ana tsananin bukatarsa".

Wani mai shago Sayed Rahman, ya shaidawa Reuters cewa shagonsa ya lalace, inda ya ce: "Ban taba ganin mummunan hari ba a rayuwata kamar wannan."

Wani mazaunin garin Abdul wahid, ya shaidawa BBC cewa tashin bam din "kamar girgizar kasa ne"

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Mutane sun taru a wajen da lamarin ya faru cikin tashin hankali don neman 'yan uwansu

Su waye suka mutu a harin?

 • BBC ta tabbatar da cewa, Mohammed Nazir, wanda yake aiki da BBC a matsayin direba fiye da shekara hudu ya mutu a harin. Sannan kuma hudu daga cikin abokan aikinsa sun ji rauni. Sai dai raunin nasu ba mai tsananin da ake tsammata musu mutuwa ba ne.
 • Ministan harkokin wajen Jamus Minister Sigmar Gabriel ya ce ma'aikatan ofishin jakadancin kasar sun jikkata kuma wani mai gadin ofishin dan Afghanistan ya mutu.
 • Jami'an Faransa sun ce harin ya lalata ofishin jakadancin kasar amma ba wani ma'aikacinsu da ya mutu ko ya ji rauni.
 • Ofishin jakadancin Birtaniya ya ce babu wani ma'aikacinsu da ya bace.
 • Ministan harkokin wajen Indiya Sushma Swaraj ya ce ba abin da ya sami ma'aikatansu.
 • Wasu ma'aikatan ofishin jakadancin Japan sun samu raunuka.
 • Turkiyya ta ce ofishin jakadancinta ya lalace amma babu wanda ya jikkata.
 • Kamfanin dillancin labarai na Afghanistan Tolo news agency ya sanya a shafin Twitter cewa maa'ikacinsu daya Aziz Navin ya mutu.
 • Wani dan jaridar kamfanin Tolo ya ce mafi yawan wadanda suka mutun ma'aikatan kamfani waya na Roshan ne, amma ba a tabbatar ba a hukumance tukunna.
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Wakilin BBC Justin Rowlatt ya ziyarci wajen da aka kai hari a watan Afrilu

Manyan hare-haren da aka kai Kabul a baya-bayan nan

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Harin da aka kai masallacin Baqir ul Olum a watan Nuwambar 2016
 • 8 ga Maris 2017 - Fiye da mutum 30 sun mutu bayan wasu mahara sun yi shigar likitoci suka kai hari asibitin sojoji na Sardar Daud Khan
 • 21 ga Nuwamba 2016 - A kalla mutum 27 ne suka mutu a wani harin kunar bakin wake da aka kai masallacin Baqir ul Olum lokacin wani taron 'yan Shi'a
 • 23 ga Yuli 2016 - A kalla mutum 80 ne suka mutu a wasu tagwayen hare-haren bam da aka kai kan wasu 'yan Shi'a da suke tattaki a dandalin Deh Mazang
 • 19 ga Afrilu 2016 - A kalla mutum 28 ne suka mutu a wani babban harin bam da aka kai kusa da ma'aikatar tsaro ta Afghanistan
 • 1 ga Fabrairu 2016 - Mutum 20 sun mutu a wani harin kunar bakin wake da aka kai hedikwatar 'yan sanda
 • 7 ga Agusta 2015 - A kalla mutum 35 ne suka mutu a wasu hare-haren bam da aka kai a yankuna daban-daban na Kabul

Labarai masu alaka

Karin bayani