Nigeria: Majalisa ta amince da kudurin goyon bayan yaki da cin hanci

Majalisa Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Majalisa za ta mara wa yaki da cin hanci da rashawar Buhari

A Najeriya Majalisar dattawa ta amince da wani kudurin doka da zai karfafa yakin da gwamnatin Shugaba Muhamadu Buhari take yi da cin hanci da rashawa a kasar.

Kudurin dokar ya amincewa hukumomi su hada karfi da karfe da takwarorinsu na kasashen waje wajen kwato kadadorin da aka saya da kudaden haram ko kudaden kasar da aka sace da aka kai kasashen waje.

Sanata David Umar shi ne shugaban kwamitin sharia na Majalisar Dattawa kuma a hirarsa da BBC ya ce, "Wannan kuduri ne da ya bayar da dama ga Najeriya da sauran kasashe su yi cudanya, ta hanyar taimaka wa juna domin a samu hujjoji da za a yi amfani da su a shari'ar da ake yi, ko kuma za a gabatar."

"A ko wacce kasa akwai wannan cudanya tsakaninsu, idan akwai shari'ar da ake bincike a kan cewa an yi laifi, a wannan kasar ko kuma a Najeriya, to wannan kasar ko kuma Najeriyar za ta iya neman taimakon waccar kasar da ta taimaka mata ta samu shaidu, ko shaida, ko mai bayar da shaida, wanda zai zo ya bada shaida domin a samu cimma burin wannan shari'ar da ake yi" in ji shi.

Da aka tambaye batun kudaden da aka sata ko kadarorin da aka saya da kudaden da aka sata, aka kuma boye a wasu kasashen, sai ya ce: "Najeriya za ta iya nema daga kasashen da ake zargin an boye wadannan kudude, domin a binciko wadannan kudaden domin a samu a dawo da su, kamar yadda aka tsara"

Dangane da tasirin da kudurin ke da shi dangane da yunkurin da gwamnati ke yi, na yaki da cin hanci da rasahawa idan aka amince da shi, sai ya kara da cewa: " Zai taimaka kwarai da gaske domin akwai kasashe da dama wanda ba a iya samun a shiga domin a nemi irin wadandan shaidu da kuma taimako, yanzu idan an amince da wannan kuduri zai ba da dama a samu wannan taimakon, wanda za a dawo da kudaden da aka ce an kwashe daga nan".

Labarai masu alaka