'Yan adawa sun caccaki Theresa May a muhawara

'Yan jami'iyun adawar dai sun yi ta sukar Mrs May a wajen a taron mahuwarar
Image caption 'Yan jami'iyun adawar dai sun yi ta sukar Mrs May a wajen a taron mahuwarar

Wakilan jam'iyyu bakwai a Birtaniya da za su fafata a babban zaben kasar da za'a gudanar a mako mai zuwa sun shiga wata kwarya-kwaryar muhawarar ta gidan talbijin da aka gudanar.

'Yan jami'iyun adawar dai sun yi ta sukar Mrs May a wajen a taron mahuwarar kan babban zaben da ke tafe, suna mai zarginta da rashi katabus, da kuma gujewa muhawarar mintoci 90 da aka watsa kai tsaye ta gidan talbijin.

Sakatariyar harkokin cikin gida na Burtaniyar Amber Rudd, wacce ta wakilci jam'iyar Conservatives, ta ce wani bangare na kasancewa shugaba na gari shi ne samun mukarabai masu kwazo.

'Yan siyasar sun fafata kan batutuwa da suka hada da ficewar Burtaniya daga kungiyar Tarayyar Turai, da harkokin tsaro da na shige da fice.

Jagoran babbar jam'iyar adawa ta Labour Jeremy Corbyn bai fito fili ya kalubalanci rashin halaratar Mrs May ba a lokacin da ya ke fafata wa da Ms Rudd kan batun rage kudaden da gwamnati ke kashewa.

Mr Corbyn din ya kuma fafata da shugaban jam'iyar UKIP Paul Nuttall kan batun tattallin arziki.

An dai gudanar da tambayoyi ga dukkan shugabannin jam'iyun bakwai kan tsare-tsaren su game da shugabanci.

Fira Minista May dai ta soke batun fitowa a muhawarorin gidan talabijin ne jim kadan bayan ta yi kiran a gudanar da zabe.

A ranar Laraba ne ta bayyana cewa ta gwammace ta rika karbar tambayoyi da kuma ganawa da jama'a a lokacin yakin neman zabe, a maimakon yin kace nace da sauran 'yan siyasa.

Labarai masu alaka