'Rashin abinci ya sa magungunan HIV na wahalar da mu'

Mata masu cutar HIV a Nijeriya
Image caption Matan sun ce idan sun sha maganin HIV ba abinci su kan sha matukar wahala

A Najeriya, mata masu dauke da cuta mai karya garkuwar jiki HIV na kokawa a kan rashin samun kulawa ta fannin abinci da kuma tallafi daga hukumomi don ci gaba da rayuwa.

Galibin irin wadannan mata dai za ka taras sun rasa mazajen su a sakamakon cutar ta HIV ne, tare da barin su da dawainiyar marayu.

A wata hira da BBC, wasu mata masu dauke da cutar ta HIV mai karya garkuwar jiki a jihar Kaduna da ke arewacin Nijeriyar sun ce babbar matsalar su ita ce karancin abinci.

Daya daga cikinsu ta ce a magungunan kashe karfin cutar ta HIV da ake ba su ya kan wahalar da su idan ba su ci abinci ba.

Ta kuma ce '' da mun sha maganin sai jikinmu ya dauki rawa, har wasu ma kwanciya suke yi duk kuwa saboda rashin abinci ne'',

Mata na kuma kokawa da cewa yayin da cutar ta hallaka mazajen su, 'yan uwa da kuma sauran al'umma na nuna musu tsangwama da kuma wariya.

Ita ma daya daga cikin matan ta ce bayan da mazajen nasu suka rasu babu wani wanda yake so ya sake auren su koda kuwa irin su ne masu dauke da cutar.

'' Ko ni din nan mazana uku suka rasu, babu masu son mu, kyamar mu suke yi, yawancin mu nan duka gwauraye ne bamu da mazan aure.''

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Matan sun ce suna shan wahala wajen tafiya karbar maganin saboda rashin kudin mota

Matan dai sun ce sun yi dabarar hada kan su wuri daya a matsayin kungiya inda suke taimakon junansu, amma kuma suna bukatar tallafin jari da za su rika tsayawa da kafafun su.

An dai kwashe shekaru ana yaki da cutar a Nijeriyar, musamman a jihohin da ake gani ta fi muni.

A shekarun baya, alkalumman da hukumar yaki da yaduwar cutar ta HIV/AIDS ta Najeriyar (NACA) ta fitar sun nuna cewar jihar ta Kaduna ita ce ta uku a jerin jihohin da cutar ta fi kamari.

Hukumomi jihar dai sun ce suna kokarin wanzar da shirin yaki da cutar har bayan kungiyoyi masu ba da tallafi a shirin sun tafi.

Sama da mutane miliyan 3 ke dauke da kwayoyin cutar HIV wanda ke karya garkuwar jikin dan Adam a Najeriya kuma mutane 900,000 ne kawai ke samun damar shan magani na kashe kaifin cutar a Najeriya.

Labarai masu alaka