Me ya sa tagwaye a Afirka ba su cika tsawon rai ba?

Jarirai tagwaye Hakkin mallakar hoto Science Photo Library
Image caption Kwararru a mujallar Lancet sun ce haihuwar tagwaye a yankin kudu da Saharar Afirka ta fi hadari

Daya a cikin jarirai biyar da akan haifa tagwaye a yankin kudu da Saharar Afirka na mutuwa kafin su cika shekaru biyar, kamar yadda wani sabon bincike ya bayyana a mujallar kiwon lafiya ta Lancet.

Binciken shi ne irinsa na farko da ya yi sharhi kan yawan mace-mace a tsakanin tagwaye a yankin.

Rahoton ya nuna cewa tsawon rai ga jariran da aka haifa tagwaye ya ja baya ainun akan sauran yara.

Yawan mace-mace a tsakanin jariran da aka haifa su kadai daga shekaru kasa da biyar ya ragu da rabi daga shekara ta 1995 da 2014.

Amma ga tagwayen adadin ya ragu ne da kashi daya bisa uku.

Haihuwar tagwaye na da hadarin gaske

Haihuwar tagwaye ya fi zama mafi hadari fiye da haihuwar jariri daya- ko da kuwa a ko wace kasa ne mai juna biyu za ta haihu.

Akwai karuwar hadari a haihuwar jarirai bakwaini da kuma mummunan zubar jini ga mata lokacin haihuwar.

Amma kuma kwararru sun ce wadannan hadurra sun fi faruwa sakamakon karancin kulawa da mata masu juna biyu da jariran a yankin Kudu da Saharar Afirka, inda iyaye matan kan haihu a gidajensu.

Ga misali a kasar Finland- inda ke da tsarin kulawa a fannin haihuwa mafi inganci a duniya, masu bincike sun ce a ko wace haihuwar tagwaye 1,000 akan samu 11 na mutuwa kafin su cika shekara daya.

Hakkin mallakar hoto SPL
Image caption Masana sun ce har yanzu ba a kula da barazanar da tagwaye ke fuskanta a duniya

Kwararru sun yi kira ga hukumomi da su inganta fannin kiwon lafiya a kasasen su don taimaka wa irin wadannan mata da kananan yara da ke fuskantar barazana.

Daya daga cikin masu binciken Farfesa Christiaan Monden na Jami'ar Oxford da ke ingila ya ce: '' Kawo yanzu ba a kula wa da mummunan halin da tagwaye kan shiga.''

Ya ce ya akwai bukatar gano mata masu dauke da juna biyu tun da wuri, kana su rika haihuwa a asibiti mai jami'an kiwon lafiya da suka samu horo a fannin haihuwar tagwaye.

Kazalika, a ci gaba da sa ido a kan su tun daga kwanakin farko har ya zuwa wasu watanni bayan haihuwarsu.

Amma kuma wannan wata babbar ayar tambaya ce a wasu kasashe matalauta da su ke da rauni a tsarin kiwon lafiya a duniya.

Iyalai musamman wadanda ke zaune a yankunan karkara, ba su da asibitoci a kusa da inda suke.

Akasari ba su da halin kai kan su ko da kananan asibitocin haihuwa mafi kusa, ballantana su biya kudin magani.

Ko da kuwa suna da hali, kayan aiki da kuma kwararru a fannin haihuwar tagwaye ba su da yawa kuma suna nesa da su a kasashen masu tasowa da dama.

Labarai masu alaka