Niger: Kishirwa ta kashe 'yan ci-rani 40 a hamada

'Yan ci-rani Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yawancin 'yan ci-rani na yin kasadar tafiya kasashen Turai, tsammaninsu rayuwar can ta fiye musu

Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce sama da mutum 40 ne suka ake tsammanin kishirwa ta kashesu sakamakon lalacewar da motarsu ta yi a arewacin Nijar.

Shugaban kungiyar a yankin Lawal Tahir, ya shaida wa BBC cewa, mutum shida da suka tsira daga cikinsu ne suka yi tattaki zuwa wani kauye da ke kusa, suka kai rahoton cewa, kishirwa ta kashe mutum 44 da suka hada da jarirai uku da kuma kananan yara biyu.

Ya kara da cewa, yawancin mutanen 'yan kasar Ghana da Nijar ne.

Babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da rahoton, sai dai Lawan Tahir ya ce masu bayar da agajin gaggawa sun shaida wa hukumomi, kuma tuni aka fara yunkurin gano gawawwakin mutanen.

A watan Yunin bara ma an samu gawar 'yan ci-rani 34, da suka hada da yara 20 a hamadar sahara, kusa da iyakar kasar ta Nijar da Aljeriya.

A wancan lokacin, wani ministan gwamnati ya ce, da alama kishirwa ce ta kashe su, bayan matukin motarsu ya gudu ya barsu.

Yawancin 'yan ci-ranin na zuwa Arewacin Afrika ne domin neman aiki da kuma kaucewa talaucin da ake fama da shi a kasashensu.

Karin bayani