Sudan ta hana Misrawa sana'a a Darfur

Wani sayar da kaya a kan titunan Masar Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sudan ta zargi Masar da goyon bayan 'yan tawaye

Hukumomi a kasar Sudan sun haramta wa Misrawa sayar da kayayyaki a kan titunan birnin Darfur, a yayin da dangantaka ke kara tsami tsakanin makwabtan kasashen biyu.

Dangantaka tsakanin kasashen biyu dai ta yi tsami ne bayan da Sudan ta zargi Masar din da goyon bayan 'yan tawayen Darfur. Zarge-zargen da Masar din ta sha musantawa.

Wata jarida mai zaman kanta a Sudan ta ce kwamishinan birnin El-Fasher da ke arewacin kasar, Tijani Abdallah Saleh ne ya fidda sanarwar haramcin.

A wata sanarwa ta daban da 'yan sanda suka fitar ta ce za a rika lura da 'yan kasashen waje, saboda za su iya zama masu bayar da bayanai ga 'yan tawaye.

Mista Saleh ya bayar da umarnin cewa masu sana'o'i na gida, da su nemi amincewar hukumomi kafin su bayar da hajarsu ga 'yan kasahen wajen.

Labarai masu alaka