Za a ladabtar da ɗaliba saboda yin shigar da ta bayyana tsiraici

hotunan dalibar Hakkin mallakar hoto Twitter
Image caption An yi ta yada hotunan dalibar a shafukan sada zumunta

Wata kafar yada labaran Uganda ta ce Shararriyar jami'ar Makerere ta yi barazanar ɗaukar matakan ladabtarwa kan wata daliba saboda ta sanya wani 'siket da ke nuna sassan jikinta' wanda kuma ya bayyana wani "bangare na tsiraicinta' a lokacin da daliban ke cin abincin dare.

A wata wasika da Hukumar gudanarwar jami'ar ta aike wa ɗalibar mai suna Rebbeca Nadumba, ta ce: "Ana zargin cewa hotunan da ke ci gaba da yaduwa tun ranar Juma'a da Asabar a shafukan sada zumunta na wata yarinya sanye da jar riga da siket din da aka yayyanka fale-fale wanda kuma ya bayyana tsiraici, cewa naki ne."

Wasikar ta kara da cewa in dai hakan ya tabbata, to lallai ta karya dokar jami'ar, da ta ce dalibai su yi shiga mai kamala da ta dace da al'ada", kuma kar a kawo rudani a jami'ar.

An bai wa misis Nadumba zuwa ranar Juma'a don ta yi bayanin dalilin da yasa ba a kawo ta gaban kwamitin ladabtarwar jami'ar ba kan zargin da ake mata na keta dokar sanya tufafi mai kamala a jami'ar lokacin da daliban da suka kammala karatu ke bikin murna

Har yanzu dai ɗalibar ba ta ce komai ba a kan lamarin. Sai dai kuma ɗaliban jami'ar na ta bayyana mabanbantan ra'ayoyinsu a shafin Twitter kan hukuncin da hukumar jami'ar ta dauka.

Labarai masu alaka