Manchester Utd ta sauya ra'ayinta akan Antoine Griezmann

Antoine Griezmann Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Antoine Griezmann tare da kungiyar kwallo ta Faransa domin wasan da zasu buga ranar Jumma'a da Paraguay

Kungiyar Manchester United ba ta sha'awar sayan dan wasan Atletico Madrid Antoine Griezmann.

United ta nuna sha'awarta na sayan dan wasan, har tana tunanin biyan euro miliyan 100 (Fam miliyan 87) da kungiyarsa ta gindaya idan yana son rabuwa da ita.

Amma wata majiya mai kusanci da United ta bayyana cewa Griezmann mai shekaru 26 da haihuwa baya cikin wadanda suke zawarci a yanzu.

An fahimci cewa United na bukatar wani dan wasa saboda Zlatan Ibrahimovic na fama da rauni na lokaci mai tsawo, kuma akwai shakku idan dan asalin kasar Sweden din zai cigaba da zama a United bayan karewar kwantaraginsa a karshen watan Yuni.

Ba a yanke wani hukunci ba game da halin da Ibrahimovic yake ciki, amma tun da ba zai buga wani wasa ba har sai watan Janairu, da wuya a iya sabunta kwantaraginsa.

Ana ganin kungiyar United na neman dan wasan gaba ne yanzu, ba dan wasa mai lamba 10 ba, domin suna da isassun 'yan wasa a wannan wurin.

Kotun sulhu ta wasanni ta tabbatar da hukuncin dakatarwar da aka yi ma kungiyar Atletico, dalilin da zai hana ta maye gurbin Griezmann da wani dan wasan idan har ya bar kungiyar kafin watan Janairu.

Labarai masu alaka

Karin bayani

Labaran BBC

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba