An sa wa Jacob Zuma 'ido' a Afirka Ta Kudu

Jacob Zuma
Image caption Dama dai Jacob Zuma na fuskantar matsin lamba daga Majalisar Dokokin kasar

Shugaban Afirka ta Kudu, Jacob Zuma, na fuskantar wani sabon sa-ido, bayan da aka tsegunta wasu sakwannin email, wadanda aka yi zargin cewa sun bayyana wani jerin ayyukan rashawa tsakaninsa da zuri'ar attajiran nan ta Gupta.

Takardun da aka wallafa a jaridun kasar Afirka ta Kudu, sun nuna cewa an bai wa iyalan na Gupta, kudaden da za su iya haura dala miliyan 400 a wata yarjejeniya, domin sayen injinan jiragen kasa kirar China wa kamfanin sufurin jiragen kasa na gwamnatin Afirka ta Kudu.

Sakwannin na email dai sun nuna girman yadda iyalan na Gupta masu janyo cece-ku-ce ke rike da akalar Shugaba Zuma da ministocinsa da kuma cibiyoyi na gwamnati.

Iyalan na Gupta dai ba su mayar da martani ga zarge-zargen ba, amma mai magana da yawun Shugaba Zuma ya bayyana su a matsayin kage.

Labarai masu alaka