'Adana ƙwan mahaifata ya taimaka min bayan fyaɗe'

picture of Winnie at a red carpet event Hakkin mallakar hoto Winnie M Li
Image caption Winnie a wajen taron ba da kambu na fim kafin rayuwarta ta sauya

Winnie Li ta zauna a Landan a lokacin tana da shekara 29, inda take zaune cikin rufin asiri da jin dadi a matsayin mai shirya fim, inda take aiki da taurarin fim kamar Daniel Craig.

Ta samu nasarar lashe kyautar "Oscars," a lokacin da aka gabatar da wani fim da ta taimaka wajen shiryawa.

Sai dai a shekarar 2008 ne al'amuranta suka tsaya cak. A ranar wata Asabar ne aka yi mata fyade a lokacin da take shawagi a arewacin Ireland.

Ta ce wannan wani abu ne wanda ba za ta taba mantawa ba, kuma bakin-cikin abin ba zai fita daga ranta ba.

Ta shaida wa BBC cewa, "Wannan wani al'amari ne mai ban tsoro, kasancewar ni mutum ce mai san zagayawa, na ji matukar bakin-ciki da bacin rai, na kasa samun jin dadi ko kwarin gwiwa.

'Ya ya zan zama uwa?'

Winnie ta ci gaba da zama cikin tashin hankali, inda take zaman jiran a yi shari'a.

Ta shaida wa BBC cewa, "Ba na jin kwarin gwiwa, sai dai kawai na kasance cikin fargaba na tsawon watanni.

Winnie ta shiga wahala mai tsanani, da tashin hankali da kuma zafin radadi. Idan za ta fita waje ta kasance cikin tsananin tsoron ko za a sake yi mata fyade.

Ta ce, "Har lokacin da na kai shekara 29 ina jin ba zan iya dawowa yadda nake da na gudanar da harkokina ba."

Wannan halin da ta shiga ya shafi rayuwarta ta samun mijin aure.

"Duk sauran kawayena sun ci gaba da gudanar da harkokin rayuwarsu, wasu sun yi aure har ma sun haihu," in ji ta.

Har a shekarar da ta gabata da ta cika shekara 37 a duniya ba ta sami mijin aure ba.

Hakkin mallakar hoto Winne M Li

Ta ce, " A wannan shekaru ne mutane suke gargadinka kan cewa kwan haihuwar mace na yin kasa, kuma babu wata hanya da za ki bi ki zama na uwa."

Gano hakan ne ya sa ta yi shawarar daskarar da kwayayen haihuwarta na mahiafa.

An yi mata aikin daskarar da adana kwan mahaifar har sau biyu. Ko da yake likitoci sun yi kokarin adana wasu kwayayen mahaifar tata, amma ba lallai su isheta ba saboda shirin tsarin inshorar lafiya ba zai ba ta dama a yi mata na uku ba.

"Mata da yawa suna ganin adana daskararren kwayayen a matsayin wani abu mai ma'ana. Amma ta wani bangaren ba haka ba ne. Na kashe makudan fama-famai," in ji ta.

Ta ce ba za ta iya biya a yi mata a karo na uku ba.

Winnnie ta kara da cewa, "Ba lallai ba ne ya ba ni kwarin gwiwa, amma zai ba ni dama na gani ko kwayayen za su taimaka min in haihu a lokacin da na yi aure."

"Na san cewa ko yanzu na yi iya kokarina a wannan fannin."

Winnie ta rubuta wani littafi mai taken, "Dark Chapter", inda ta bayyana abubuwan da ta fahimta dangane da fyade da kuma hanyoyin magancewa.

Hakkin mallakar hoto Winnie M Li
Image caption Winnie ta ci gaba da fita shawaginta yadda ta saba

Har ila yau, tana karatun digirin-digirgir a wata makarantar koyar da tattalin arziki ta Landan, inda ta binciko yadda shafukan sada zumuntar zamani suke bayar da dama ga wadanda suka tsira daga fyaden da akai musu wajen bayyana labarunsu.

"Ko wacce rana ina daukar darasi daga wurin matan da suke fama irin wannan matsalar na yadda suka manta da komai suka ci gaba da rayuwarsu.

"Ina fatan daga wadannan labaran da na wallafa, za mu fahimci yadda za mu magance irin wannan radadin," In ji ta.

Labarai masu alaka

Karin bayani