Kalli hotunan layin dogon da zai ratsa ƙasashen gabashin Afirka

Kasar Kenya ta kaddamar da sabon layin dogo da zai hada birnin Mombasa da babban birnin kasar Nairobi.

Train Hakkin mallakar hoto Michael Khateli

Layin dogon wanda kasar Sin ce ta gina shi, ya lashe dala biliyan 3.2 kuma shi ne babban ci gaba da kasar ta samu tun samun 'yancin kai. Wani kamfanin kasar Sin ne ya gina shi kuma yawancin direbobin da injiniyoyin duk 'yan kasar Sin ne tun farkon fara amfani da shi, sannan daga bisani 'yan kasar ta Kenyan za su ci gaba da tafiyar da ayyukan sarrafa jirgin. Daga Nairobi zuwa Mombasa jirgin zai rika tafiyar sa'a hudu da rabi, a maimakon sa'o'i tara da motar bas take dauka ko sa'o'i 12 da tsohon jirgin kasa yake dauka kafin ya isa.

Interior of train Hakkin mallakar hoto Michael Khateli

A yanzu dai tsawon layin dogon ya kai kilomita 472. Amma shirin na tsawon shekara 25 ne da za a ci gaba da yi wanda zai wuce har zuwa kasashen Sudan Ta Kudu da Rwanda da Burundi da Ethiopia da Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo kuma har zuwa tekun Indiya. An dauki tsawon shekara uku da rabi ana gina layin dogon, inda aka yi amfani da kayan fasahar zamani na ksar China. Layin dogon ya ratsa gadoji 79 yana kuma da manyan tasoshi biyu da kananan tasoshi bakwai da tasoshin da zai dinga tsaya na wucin gadi 23.

Railway tracks Hakkin mallakar hoto Michael Khateli

Ko wacce tasha ta layin dogon da ake kira da Madaraka Express, an gina ta ne yadda za ta dace da yanayin wajen. An gina tashar Athi da ke bakin kogi da zummar a dinga hango tsaunukan da ke kusa da yankin, ita kuwa tashar Miasenyi da ke kusa da daji za a dinga hango jakan dawa daga wajen.

Mombasa station Hakkin mallakar hoto Michael Khateli

Babbar tashar jirgin da ke Mombasa kuwa an yi ta ne ta yadda za a dinga ganin kamar ruwa.

Detail from Mombasa station Hakkin mallakar hoto Michael Khateli
Detail of station Hakkin mallakar hoto Michael Khateli

Su kuwa turakun da suke wajen an yi su ne don su zama kamar igiyar teku.

Platforms at Mombasa station Hakkin mallakar hoto Michael Khateli

Nairobi ce babbar tashar jirgin. A nan ne kuma za a dinga ajiye kayan gyaran jirgin. Sun yi kama da wasu injina biyu da suke tunkarar juna.

Nairobi station Hakkin mallakar hoto Michael Khateli
Walk to railway platform Hakkin mallakar hoto Michael Khateli
Interior of building Hakkin mallakar hoto Michael Khateli

Michael Khateli ne ya dauki hotunan

Labaran BBC