Nigeria: Ce-ce-ku-ce ya kaure kan kafa hukumar raya yankin Igbo

Majalisar wakilan najeriya Hakkin mallakar hoto National Assembly
Image caption 'Yan Majalisar wakilan Najeriya da suka fito daga Kudu maso Gabashin kasar sun ce za su sake gabatar da kudurin gaban majalisa

Ce-ce-ku-ce ya kaure a majalisar wakilan Najeriya bayan ta yi watsi da kudirin kafa hukumar raya yankin Kudu maso Gabashin kasar, inda ake fafutikar kafa kasar Biafra.

Da farko an nemi a jingine kudirin ne domin wanda zai jagorance shi bai bayyana gaban majalisar ba.

Amman 'yan majalisar wakilan Najeriya da suka fito daga yankin kudu maso gabashin kasar ba su ji dadin hakan ba lamarin da ya sa aka shiga hargitsi a majalisar.

Daga baya dai an gabatar da kudurin tare da bayyana irin yadda zai sa mutanen kudu maso gabashin Najeriyar su ji ana son su a kasar.

Sai dai kuma wasu 'yan majalisar kasar sun ce idan aka yarda da kudurin, ko wace shiyyar kasar za ta nemi a kafa mata hukumar raya ta.

Daga bisani, kakakin majalisar, Yakubu Dogara, ya nemi 'yan majalisar su kada kuri'a ta baka kan kudirin inda wadanda suka ki amicewa da shi suka samu rinjaye.

Amman 'yan majalisar da suka fito daga shiyyar kudu maso gabashin kasar ba su yarda da sakamakon zaben ba, suna masu cewa ba a yi musu adalci ba.

A wani jawabin da suka yi wa manema labara cikin gaggawa bayan sun fice daga zauren majalisar domin nuna rashin amincewarsu da zaben, 'yan majalisar wakilan Najeriyar da suka fito daga yankin sun ce za su sake dawowa da kudurin.

"Wanda ya jagoranci zaman majalisar ne ya kashe kudirinnan. Wadanda suka ce E sun fi yawa. Dan uwa na ne, amman na ji matukar takaicin abin da ya faru yau," in ji daya cikinsu.

Ya kara da cewa: "Wannan wani kudiri ne mara cutarwa, ba zai dami kowa ba. Me ya sa za a kashe shi?

"Za mu daukaka batun, za mu kai gaba. Za mu soke shi mu sake dawo da shi. Kuma za mu ci gaba da zuwa har sai mun samu abinda muke so."

Masu sharhi na ganin wannan lamari ka iya kawo rabuwar kawuna a majalisar.

Labarai masu alaka