Duniya ta caccaki Trump kan yarjejeniyar Paris

Donald Trump Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Shugaba Trump ya ce yarjejeniyar za ta yi nakasu ga tattalin arzikin Amurka

Kasashen duniya sun yi Allah-wadan ficewar Amurka daga yarjejeniyar yanayi ta Paris wadda shugaba Donald Trump ya sanar ranar Alhamis.

Firamin Ministar Birtaniya, Theresa May, ta shaida wa Shugaba Donad Trump takaicinta kan shawarar ficewa daga yarjjeniyar yanayin Paris da ya yanka.

Wata sanarwar da fadar Downin Street ta fitar ta ce a tattaunawarta da shugaba Trump ta wayar tarho, Firayim ministar Birtaniyar ta ce yarjejeniyar Paris din ce ta ba da tsarin duniya na kare ci gaba da kuma tsaron karni na gaba baya ga samar da makamashi mai rahusa ga mutane da kuma kamfanoni.

Kungiyar tarayyar Turai ta ce ranar Alhamis wata ranar bakin ciki ce ga duniya, amman ita za ta ci gaba da yakar dumamar yanayi domin tarihi na bayanta.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu zangangar kin matakin da Shugaba Trump ya dauka kan yarjejeniyar yanayin Paris sun hallara a gaban fadar White House

Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya ce Faransa ba za ta sake wata sabuwar yarjejeniya kan yarjejeniyar ba.

Ya ce: "A wannan yammaci, zan shaida muku da kakkausar lafazi: ba za mu sake tattaunawa domin samun yarjejeniya mai karamar manufa ba ko ta yaya. A wanna yammaci, Faransa ta yi kira ga dukkan kasashen da suka rattaba hannu su tsaya kan yarjejeniyar Paris, kuma su kiyaye iya nauyin da suka rataya wa kansu kuma kar su rage komai."

Duk da cewar kungiyar da rajin kare hakkin masu makamashin kwal a Amurka ta yi maraba da matakin shugaba Trump din, gwamnonin jihohin Washington da New York da kuma Carlifornia tare da magadan gari a biranan Amurka 61 sun saba wa hukuncin da shugaban ya yanka, kuma sun lashi tkwabin yakar dumamar yanayi.

Sai dai kuma babu tabbacin irin tasirin gwamnoni da kuma magadan garin za su yi kan dumamar yanayi.

Labarai masu alaka