An samu raguwar mutuwar yara saboda cutar gudawa

Fiye da kashi arba'in na yaran da ke mutuwa sun fito ne daga Nigeria da kuma India
Image caption Fiye da kashi arba'in na yaran da ke mutuwa sun fito ne daga Nigeria da kuma India

Wani sabon bincike da aka gudanar ya nuna cewa an samu raguwar adadin mutuwar kananan yara sakamakon cutar gudawa da kusan kashi uku as tsakanin shekarun 2005 da 2015.

A sakamakon da aka wallafa a mujallar kiwon lafiya ta The Lancet, masu binciken daga Amurka sun ce mai yiwuwa an samu wannan ci gaba ne saboda samun ruwan sha mai kyau da kula da tsabtar muhalli da kuma raguwar kananan yara dake fama da Tamowa.

Duk da nasarorin da ake samu wajen magance gudawa, har yanzu cutar ce ta hudu cikin jerin cututtuka masu hallaka kananan yara a duniya, inda cutar ke sanadiyar mutuwar kananan yara 'yan kasa da shekaru biyar kusan dubu dari biyar a kowace shekara a fadin duniya.

Fiye da kashi arba'in na yaran da ke mutuwa dai sun fito ne daga Nigeria da kuma India.