Ana ƙera jirgin ruwa mai amfani da lantarki zalla

Jirgin ruwan da ba zai rika fitar da hayaki ko kadan ba Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jirgin ruwan da ba zai rika fitar da hayaki ko kadan ba

Wani kamfani a kasar Norway ya ce yana ƙera wani katafaren jirgin ruwa da ya yi amannar cewa shi ne irinsa na farko da zai rika amfani da wutan lantarki zalla ba tare da wani inji na ko-ta-kwana ba.

Jirgin ruwan da ba zai rika fitar da hayaki ko kadan ba, idan an kammala shi a watan Afrilu mai zuwa zai iya kwasar fasinjoji 400 a yammacin Norway.

Shugaban kamfanin Rolf Sandvik, ya shaida wa BBC cewa jirgin zai rage gurbatar muhalli, a wani yanki da Hukumar Raya Ilmi da Kimiya da Al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya, UNESCO ta ware.

Ya kara da cewa yana fatan a matsayin shi na dan kasuwa, nan gaba Shugaba Trump wata rana zai fahimci cewa akwai matukar tasiri ta fuskar kasuwanci a rika daukar batun kula da yanayi da matukar muhimmanci.