Wasu sun yaɗa hoton ƙarya na shugaban ƙasar Senegal 'tsirara'

Tun shekarar 2012 shugaban yake mulki Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tun shekarar 2012 shugaban yake mulki

Majiyar 'yan sanda ta shaida wa BBC cewa, an kama mutum hudu 'yan kasar Senegal da suka dauki hoton shugaban kasar, Macky Sall, na bogi a tsirara, kuma suka yada shi a shafukan sada zumaunta.

Majiyar ta ce, a ranar Lahadi ne aka kama wata matashiya 'yar jarida da ake zargin ita ce ta fara yada hoton shugaban, sauran mutum ukun kuma aka kama su a ranar Laraba.

Sai dai kawo yanzu mutanen da aka kama ba suce komai ba.

Majiyar ta ce, har ana ci gaba da bincike, sai dai wadanda suke da hannu a ciki za a iya tuhumarsu da laifukan "Yada hotunan batsa" da kuma "Muzanta shugaban kasar".

'Yar jaridar tana aiki ne a gidan talabijin na Touba, mallakar darikar Mouride, darikar addinin Musulunci ta biyu mafi girma a kasar.

Hankalin wasu daga cikin wadanda suka ga hoton yi yi matukar tashi.

Sai dai wasu sun yi tur da hukumomi a bisa abin da suka kira yunkurin tauye 'yancin fadin albarkacin baki.

Labarai masu alaka