An yanke hukuncin kisa ga wanda ya yi fyade

Shugaban kasar Masar Abdel Fattah el-Sisi

An yanke wa wani dan kasar Masar hukuncin kisa kan aikata fyade.

Wata majiyar shari'a, ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa wata kotu a kasar Masar ta yanke wa wani mutum da ya yi wa yarinya 'yar wata 20 fyade hukuncin kisa.

Mahaifiyar yarinyar ta tuhumi mutumin mai shekaru 35 da haihuwa da yin garkuwa da 'yarta kuma ya yi mata fyade, sanadin da ya haddasa wa yarinyar mummunan zubar jini.

A watan Maris ne hukumomi suka kama mutumin.

Yana da damar daukaka kara a kan hukuncin da aka yanke masa a babbar kotun kasar,