Najeriya: Bikin kayan gyaran gashi

Jerin kayan gyaran gashi na mata a wajen babban taron albarkatun gashi na Afirka a Abuja, Najeriya yau 2 ga watan Mayu 2017

Ana taron koli a kan albarkatun kayan gyaran gashi na Afirka a Abuja, babban birnin Najeriya.

Kungiyar Photizo Life Foundation ce take shirya taron wanda ake yin sa a kowace shekara, domin "tabbatar da lafiyar tunani da na zamantakewar al'umma".

Kungiyar ta ce ta shirya taron ne domin sanar da jama'a game da hatsarin amfani da kayan gyaran gashi masu cutarwa, kuma a karfafa masu alfanun amfani da kayan gyaran gashi na gida domin, "tallata al'adun mutanen Afirka".

Chris Ewokor na BBC, wanda yake halartar taron ya aiko mana da wadannan hotunan.