Ko ya dace mata su shiga harkar siyasa?
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ko ya dace mata su shiga harkar siyasa?

Da yawa daga cikin mutanen da suke yankin arewa maso gabashin Najeriya, sun yi mamaki a lokacin da Hajia Aisha Alhassan ta fito takarar gwamnan jihar Taraba, a lokacin zaben shekarar 2015, wacce kuma a yanzu ita ce ministar harkokin mata.

Mun ji dadi da jajircewarta da kuma tsayawa tsayin daka na shiga fagen fama. Muna matukar alfahari da namijin kokarin da ta yi.

Ta bai wa mara da kunya da 'yan adawa, muna matukar alfahari, sannan kuma muna jin ba dadi game da abubuwan da ake nunawa mata 'yan siyasa a arewacin Najeriya.

Mun san cewa ta cancanci zama gwamna, sai dai kuma akwai barazanar fuskantar matsaloli a yanayin tafiyar da harkokin gwamnati a jihar Taraba.

Daya daga cikin babban kalubale da za ta fuskanta shi ne, tasirin al'ada a kan shugabancin mace, sai kuma bangaren tarihi.

Ko da yake manazarta na da bambancin ra'ayi, wasu na ganin cewa bai dace mace ta yi shugabanci ba musamman ma a matsayin gwamna. Wadannan mutane sun dogara ne a kan fahimtarsu inda suke ganin cewa babban laifi ne wanda ya kamata a ce ka tuba idan ka ce mace ta jagoranci gwamnati.

Har ila yau, akwai wasu bangaren da suke kalubalantar cewa mace za ta iya zama gwamna matukar ba gwamnatin Musulunci ba ce.

Suna ganin cewa kasar da ake amfani da tsarin shari'ar Musulunci ne kawai aka haramtawa hakan. Inda suka buga misali da labarin sarauniya Sheba wato Bilkisu mai gadon zinare.

Image caption Aisha Alhassan tana gwagwarmaya a fagen siyasar Najeriya

Sun yi amanna cewa matukar kasar tsarin dimokaradiyya ake bi to mace tana da damar tsayawa ko wacce irin takara.

Bakuwarmu a wannan fili, Sanata Binta Masi Garba, ta fuskanci irin wannan matsalolin ta nuna fifikon jinsi, da nuna wariya na cikin al'adar siyasar, ta yi takara kuma ta samu nasara, inda ta lashe kujerar majalisar dokoki.

Ta fada min cewa, kasancewa mace a harkokin siyasar Najeriya musamman ma idan macen 'yar arewa ce, to za ki fuskanci kalubale da dama.

A cewarta mutanenmu sun dauki macen da take siyasa a matsayin mara tarbiyya, da kuma rashin kamun kai. A lokacin da ta yi takara a jihar Kaduna da Adamawa, tana da yakinin cewa ta samu nasara, saboda ta samu damar da ta tsallake dukkan wadannan turakun, a matsayinta na uwa.

Sanata Binta Masi Garba da Haj. Aisha Alhassan sun zama mata masu kamar maza.

Nima Fatima Zahra Umar, zan iya shiga siyasa don mu tabbatar wa da duniya cewa, akwai matan da a shirye suke su kawo wa kasarsu ci gaba.

Sun share mana hanya, kuma nima zan yi takarar gwamna a jihar Adamawa a zaben shekarar 2019! Na tabbata cewa mata za su taka muhimmiyar rawa a harkokin gwamnati, kasancewar su ne iyayen al'umma, mune muka fi dacewa da sanin abubuwan da al'ummarmu suka fi bukata, da kuma kirkiro wasu hanyoyin da za su magance matsaloli fiye da maza.

A gaskiya, maza sun faye son kansu.

Ya kamata mu tambayi kanmu, a matsayinmu na al'umma, shin me yasa muke fushi idan aka ce mace ce za ta iya zama shugabar kasa? A ce dai Hajiya ce shugabar kasa! Wata kila wata rana a Najeriya a samu 'gentleman' mijin shugabar kasa maimaikon 'first lady da aka saba samu matar shugaban kasa!

Labarai masu alaka