Annobar murar tsuntsaye ta ɓulla Nigeria

Wasu kaji Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Baya ga hallaka tsuntsaye, wani nau'in cutar murar tsuntsaye na iya kama ɗan adam.

A samu rahoton sake ɓullar cutar murar tsuntsaye wato Bird Flu a wasu jihohi biyar da ke Najeriya.

Jihohin sun hada Kano da Filato da Bauchi da Babban Birnin Tarayya Abuja da kuma Jihar Kaduna.

Wani jami'i mai kula da lamarin a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin kasar Dokta Abel William ya shaida wa wakilinmu cewar an samu bullar cutar a jihar ne a gonaki uku.

Sakataren kungiyar masu kiwon kaji a jihar Kano, Umar Kibiya, ya tabbatar da bullowar cutar kuma ya ce cutar ta karya jarin manoma da dama a shekarar 2015 inda har yanzu suna jiran kudin diyyan da gwamantin kasar ta yi alkawarin biyansu domin su koma kiwo.

Matakin da aka dauka a Kano da Kaduna

Sakataren ya ce ya sanar da mambobin kungiyarsu game da barkewar annobar. Har ila yau, ya ce "na ye musu kowa ya kara tsare gonarsa, ya kuma kara tabbatar da tsaftar gonarsa". Hakazalika, ya ce kungiyarsu tana shirya taron wayar da kan jama'a kan yadda za su kare gonakinsu da yadda za su yi mu'amala da tsuntsaye da kuma hanyoyin rigakafi.

Dokta William ya ce. "Yanzu gwamnatin jihar Kaduna ta ba da umarnin a sayo wasu magunguna don a bai wa masu gonar kaji su ringa sanyawa a gonakinsu. Har ila yau, gwamnatin ta sa an fara wayar da kan masu gonaki don fahimatar matsalar," inji shi.

Cutar wacce cikin hanzari kan kashe kaji musamman a gidajen gona ta haifar da asara mai yawa ga masu gidajen gona a jihohi da dama a Najeriya a shekarar 2015, inda har yanzu wasu masu kiwon kaji ke cewa ba a biya su diyyar da gwamnati ta yi alkawarin biyan su ba.

Labarai masu alaka