'Kafin ka shiga Amurka sai an ga tarihinka na Facebook'

Za a iya bukatar masu neman takardar iznin shiga Amurka su gabatar da sunayensu na shafukan sada zumunta da lambobin waya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Za a iya bukatar masu neman takardar iznin shiga Amurka su gabatar da sunayensu na shafukan sada zumunta da lambobin waya

Gwamnatin Donald Trump ta amince da wani tsari da zai bukaci masu neman takardar iznin shiga kasar su yi bayanin yadda suke amfani da shafukan sada zumunta.

Daga cikin tambayoyin da jami'ai a ofishin jakadancin kasar za su bukata har da neman karin bayani kan sunan da mutum yake amfani da shi a shafukan sada zumunta tun daga shekaru biyar da suka gabata.

Hakan na nufin hukumomi za su nemi adireshin Email da lambobin waya da kuma bayani dalla-dalla na wasu shekaru 15.

Wani jami'i a ma'aikatar harkokin kasashen wajen Amurka ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, za a bukaci wadannan bayanai ne matukar ana neman tantance batun tsaron kasa.

Sai dai masu sukar matakin sun ce wannan binciken kwa-kwaf zai janyo bata lokaci wajen neman wasu bayanai da ba su da muhimmanci.

Labarai masu alaka